logo

HAUSA

Ta yaya kananan yara da matasa za su motsa jiki ta hanyar kimiyya?

2023-02-04 15:29:46 CMG Hausa

Matasa da kananan yara suna girma a ko wace rana. Motsa jiki ta hanyar kimiyya da kuma cin abubuwa masu gina jiki suna taimaka musu wajen kyautata karfin garkuwar jiki, da kara yadda suke girma. Masana sun ba da shawarar cewa, ya kamata a mai da hankali kan cin abubuwa masu gina jiki, motsa jiki ta hanyar kimiyya, da samun isasshen barci don samun isashen kuzari, a kokarin ganin matasa da kananan yara sun girma yadda ake fata.

A lokacin kuruciya da na yarantaka, girman kashin wasu mutane na daukar lokaci, musamman ma kashin hannaye da kafafu a lokacin da shekaru suka kai 12 zuwa 18 a duniya. Don haka matasa da kananan yara suna bukatar samun abubuwa masu kunshe da furotin, sinadarin Calcium da sinadarin phosphorus daga dukkan fannoni, kana ya kamata su rika cin nama maras kitse, kwai, madara, kifi yadda suke bukata, da kuma wake, hatsi, da sauran abubuwa masu kunshe da bitamin B da E wadanda suke taimakawa wajen kyautata yanayin sarrafa sinadaran jiki, ta yadda kashin mutane za su girma yadda ya kamata.

Motsa jiki ta hanyar da ta dace, yana taimakawa matasa da kananan yara su shigar da sinadarin Calcium da sinadarin phosphorus, kara saurin girman kashinsu. Har ila yau motsa jiki yana inganta gudanar jini a jikin dan Adam baki daya, lamarin da ya sanya dukkan sassan kashin dan Ada, su samu isasshen abubuwa masu gina jiki, ta haka kashin dan Adam suke girma cikin sauri.

Masana suna bai wa matasa da kananan yara shawarar yin tsalle-tsalle, hawan sanda, hawan makakaklar da aka yi da igiya, yin wasan tsalle da igiya, yin wasan ninkaya da dai sauransu, a kokarin kara juriyar gwiwa, da jijiyoyi da suka hada kasusuwa biyu, ta yadda za su yi girma yadda ya kamata. Amma bai kamata matasa da kananan yara su rika yin wasan daukar kayan nauyi ko sandar karfe, yin wasan jifan dalma ko kayan karfe da dai makamantansu.

Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, ya fi kyau kananan yara da matasa su rika motsa jiki sau 2 ko 3 a ko wane mako, kuma mintoci 30 zuwa 60 a ko wane lokaci. Motsa jiki yadda ya kamata na kara azama kan girman kasusuwansu, amma motsa jiki fiye da kima, yana kawo illa ga yadda kasusuwansu ke girma yadda ya kamata, musamman ma yin tsalle-tsalle da dama kan kasa mai tsauri. Kana kuma kamata ya yi a kare kananan yara da matasa daga daukar tsawon lokaci suna motsa jiki tare da abubuwa masu nauyi, saboda motsa jiki tare da abubuwa masu nauyi cikin dogon lokaci kan illanta lafiyar kashin kafaffunsu.(Tasallah Yuan)