logo

HAUSA

An gabatar da shirin tallata bikin fitilu na gargajiyar Sin a Afrika ta Kudu da Habasha

2023-02-04 15:45:14 CMG Hausa

An gabatar da shirin fim na tallata bikin fitilu na gargajiya na kasar Sin, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya shirya, a dandalin taro na Nelson Mandela, wanda ke zaman muhimmin gini a Johannesburg, birni mafi girma a Afrika ta kudu.

Wannan shi ne karon farko da aka nuna irin wannan shiri na bikin fitilu da CMG ya shirya a wani wurin taron jama’a a Afrika ta kudu. Shirin wanda aka haska a babban majigi, ya ja hankalin masu yawon bude ido. Haka kuma, Sinawa mazauna birnin sun kai abinci na musamma ga ‘yan kasar Afrika ta kudu dake dandalin, inda suka rika musu bayani game da bikin na fitilu.

Akwai Sinawa 300,000 dake zaune a kasar ta Afrika ta kudu. Kuma haska shirin tallata bikin fitilu na kasar Sin ya sa Sinawan jin tamkar suna gida. Sun kuma ce nuna shagulgulan murnar bikin bazara da bikin fitilu na gargajiyar kasar Sin da CMG ya shirya, sun nishadantar da Sinawa dake zaune a kasashen waje.

Har ila yau a jiyan, an gabatar da shirin tallata bikin fitilu na kasar Sin a dandalin Meskel na kasar Habasha. Shi ne kuma karon farko da aka nuna bikin a babban majigi ga jama’a a kasar ta Habasha. (Fa’iza Mustapha)