Sin ta yi bayani game da dage ziyarar sakataren harkokin wajen Amurka
2023-02-04 20:21:29 CMG Hausa
Wani babban jami’in Amurka ya bayyana cewa, sakataren harkokin wajen kasar Anthony Blinken, ya dage ziyarar da ya yi niyyar kawowa kasar Sin saboda wani kumbon kasar Sin da ya shiga sararin samaniyar Amurka.
A martaninta, kasar Sin ta ce ta nazarci lamarin kuma ta yi wa Amurka bayanin cewa, shiga sararin samaniyarta da kumbon ya yi, abu ne da ba a yi tsammani ba, kuma kumbon ba na aikin soji ba ne, ana amfani da shi ne domin binciken yanayi da sauran ayyukan da suka shafi kimiyya. Har ila yau, ta ce kumbon ya kauce hanya ne saboda karfin iska da takaitaccen iko da aike da shi kasancewarsa mara matuki. Bugu da kari, kasar Sin ta ce wannan lamari ya auku ne ba da niyya ba kuma a bayyane hakan yake karara. Haka kuma, kasar Sin ta kasance mai kiyaye dokokin kasa da kasa da girmama cikakken iko da yankunan dukkan kasashe, kuma ba ta taba keta yanki ko sararin samaniyar wata ‘yantacciyar kasa ba.
Wasu kafafen yada labarai da ‘yan siyasar Amurka suna amfani da wannan batu wajen sukar kasar Sin, abun da kasar Sin din ke adawa da shi. (Faiza Mustapha)