logo

HAUSA

An yi kira ga shugabannin Afirka da su kara azama wajen dakile harbuwar yara kanana da cutar AIDS zuwa shekarar 2030

2023-02-03 10:07:43 CMG Hausa

 

Mataimakin shugabar kasar Tanzania Philip Mpango, ya yi kira ga shugabannin kasashen Afirka, da su nuna kwarewar jagoranci, wajen sabunta kwazon kawo karshen yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki ko AIDS tsakanin yara kanana a Afirka nan zuwa shekarar 2030.

Mr. Mpango, wanda ya yi kiran yayin taron ministocin kasashen da suka shiga kawancen kasa da kasa na kawar da wannan matsala, ya ce bai kamata a yi kasa a gwiwa ba, duba da yadda wa’adin shekarar 2030 ke kara karatowa.

An dai gudanar da taron ministocin ne a cibiyar kasa da kasa ta Julius Nyerere dake birnin Dar es Salaam, kuma kasashen Afirka 12 ne ke cikin kawancen a kashi na farko na shirin. Kasashen su ne Angola, da Kamaru, da Kwadebuwa, da Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo, da Kenya. Sauran su ne Mozambique, da Najeriya, da Afirka ta Kudu, da Tanzania, da Uganda, da Zambia da kuma Zimbabwe.

Manufar kawancen dai shi ne yayatawa, da kuma ingiza yin alkawarin siyasa da albarkatu, don tabbatar da aiwatar da matakai na cimma nasarorin bai daya.  (Saminu Alhassan)