logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta yi amfani da diplomasiyya wajen yakar ’yan kungiyar Boko-Haram

2023-02-03 08:59:05 CMG Hausa

A ranar Alhamis 2 ga wata ma’aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya ta ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi amfani da dabarun huldar diplomasiyya wajen kawo karshen ayyukan ’yan Boko-Haram a yankin arewa maso yammacin kasar.

Ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyema ya tabbatar da hakan ne a birnin Abuja lokacin da yake jawabi a taron manema labarai karo na 22 wanda shugabannin ma’aikatu ke zayyana nasarorin gwamnatin shugaban kasa daga 2015-2023.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mr. Geofrey Onyema ya ce bayan zuwa gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari a shekarar 2015, matsalolin ayyukan ’yan Boko Haram ya kara ta’azzara wanda har ta kai sun mamaye wasu daga cikin yankunan kasar, wannan ya sanya shugaban   Buhari gudanar da tataunawa daban daban da shugabannin kasashen Kamaru da Chadi da Benin da kuma Jamhuriyar Nijar lamarin da ta kai ga sake sabunta shirin dakarun hadin gwiwa na yaki da ayyukan ta’addanci a yankin tafkin Chadi.

Kamar yadda minista ya fada an samu nasarar hakan ne bisa hadin kan kungiyar tarayyar Afrika da majalissar dinkin duniya.

Mr. Onyema ya ce, tun daga samar da dakarun hadin gwiwa a yankin tafkin Chadi, gwamnatin tarayyar Najeriyar ta kara samun damar kulla alakar tsaro da Amurka wanda a sanadiyar hakan Najeriya ta samu damar mallakar jiragen yaki guda 12 samfurin Super Tucano duk dai domin fatattakar ’yan ta’adda.

Haka kuma ministan ya kara da cewa a kokarin shugaban kasa ta fuskar kyautata harkar diplomasiyya da kasashen ketare, a tsakanin shekarar 2016 zuwa ta 2017 Najeriya ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da ta shafi tsaro ta 2021 da shugaba Recep Erdogan na kasar Turkiyya wanda a nan ma Najeriya ta sami damar sayen jiragen yaki masu saukar ungulu da jiragen yaki masu layar zana domin yakar ayyukan masu ta da kayar baya.

Ministan harkokin kasashen waje na Najeriya ha’ila yau ya ce a sakamakon matsalolin keta hakkin bil adama a yankin arewa maso yamma biyo bayan ayyukan dakarun hadin gwiwa, Najeriya ta samu tallafin biliyoyin dala daga kasashen Norway da Jamus bayan tsoma bakin MDD, inda aka yi amfani da kudaden wajen tsugunar da ’yan gudun hijirar yankin tafkin Chadi sama da miliyan 40 tarekuma  da ba su tallafi.

“Ba wai kawai da kasashe makwafta Najeriya ke da kyakkyawar alaka ba, tana da alaka ma da sauran kasashen duniya. Najeriya ita ce kasa daya tilo a duniya da ba a jin kanta da wasu kasashe, babu kasar da za a nuna a ce Najeriya na rigima da ita a kan kowanne abu, koda sabanin mu da kasar Kamaru a kan yankin Bakasi cikin ruwan sanyi muka warware.”

Mr. Geofry Onyema ya ce ingantaccen tsarin diplomasiyya na shugaba  Buhari ya taimaka wajen kokarin samar da tsari na duniya da zai sauya fasalin al’amura a yankin tafkin Chadi wanda yanzu haka ake aiki a kansa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)