logo

HAUSA

Qin Gang ya gana da shugaban babban taron MDD karo na 77

2023-02-03 11:05:15 CMG Hausa

Ministan wajen Sin Qin Gang, ya gana da shugaban babban taron MDD karo na 77 Korosi Csaba a jiya Alhamis a nan Beijing.

Yayin ganawar tasu, Qin Gang ya ce, kamata ya yi MDD ta kara taka muhimmiyar rawa wajen daidaita harkokin kasa da kasa. Ta kuma tsaya tsayin daka kan kiyaye zaman lafiya da tsaro, da kare adalcin kasa da kasa, da dagewa ga samun moriya tare, da kare ra’ayin bangarori daban daban bisa gaskiya, da kuma bude kofa ga kasashen waje.

Ya ce ya kamata a yi watsi da adawar akida, da inganta fahimtar juna a fannin al’adu. Kaza lika Sin za ta ci gaba da nuna goyon bayanta ga ayyukan babban taron MDD da shugaban babban taron MDD.

A nasa bangare kuwa, Mr. Korosi ya bayyana cewa, Sin muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa ce ta MDD, yana kuma godewa goyon baya da bangaren Sin ya nuna wa MDD a cikin dogon lokaci. Kazalika MDD tana dora muhimmanci kan tasiri da jagorancin Sin, ta kuma dade tana goyon bayan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. (Safiyah Ma)