logo

HAUSA

Liu Xiabing dake kokarin bunkasa sana’ar saka da gora ta gargajiya

2023-02-02 09:25:41 CMG Hausa

Masu sauraro, a makon da ya wuce, mun gabatar muku wani labari game da Liu Xiabing, ‘yar asalin garin Pingnan na gundumar Lingshan ta larin Guangxi dake kudu maso yammacin kasar Sin. Duk da cewa ta gaza sau da yawa, amma ba ta taba yin kasa a gwiwa ba, wajen bunkasa sana’ar saka ta amfani da gora. A shekarar 2016, ta soma sayar da kayan saka a yanar gizo, kuma ta gudanar da aikin yadda ya kamata. Amma, saboda ta dauki matakan da ba su dace ba, ta sake yin asara, har ma bashin da ta ci ya kai kusan RMB miliyan 2.

A cikin shirinmu na yau, za mu ci gaba da kawo muku labarinta, kuma mu duba yadda take kokarin bunkasa wannan sana’ar saka ta gargajiya.

Wata rana a cikin watan Maris na shekarar 2021, Liu Xiabing tana gabatar da samfuranta a dakin watsa shirye-shirye kai tsaye na yanar gizo. Ba zato ba tsamani, mutane da yawa sun shiga dakin watsa shirye-shiryen kai tsaye, duk suna cewa, “Sai ki yi gidan kyanwa da gora”. A yawancin lokaci, babu mutane da yawa a dakin ta, in ban da kimanin mutane sama da 20 kadan, don haka, da ganin yawan mutane kamar haka, da kuma maganarsu, Liu Xiabing ta rude sosai, ba ta san me ke faruwa ba.

Daga baya Liu Xiabing ta bi diddigin sharhin masu amfani da yanar gizo, inda a karshe ta gano dalilin. Wani ya ba da shawarar cewa, ya yi amfani da irin wannan babban kwandon 'ya'yan itace a matsayin gidan kyanwa, wanda ya dace sosai, kuma ya dauki bidiyo game da haka a yanar gizo, wanda ya jawo hankulan masu kiwon kyanwa da yawa.”

Liu Xiabing ta fahimci sosai cewa, wannan na iya zama wata dama mai kyau. Washe gari, ta je ta nemo mahaifinta, bayan tattaunawa sosai, suka tsara wani zane mai sauki game da gidan kyanwa, kuma suka ba wa wani mai saka, don ya yi samfurin, a duba ko zai iya samun karbuwa ko a’a.

A wannan rana da yamma, Liu Xiabing ta kwatanta samfurin, kuma ta yi saka a dakin watsa shirye-shiryen kai tsaye. Tana sakar gidan kyanwa a hankali, kuma masu amfani da yanar gizo suna hira da juna. Bayan sa'o'i sama da hudu, ta sayar da gidajen kyanwa kusan 200, adadin ya wuce yadda take tsammani.

Ga lokacin zuwa kwanaki 10 masu zuwa, ta sayar da gidajen kyanwa na gora yadda ya kamata, wadanda yawansu ya kai kusan 2000, inda ta samu jerin oda masu yawa har bayan tsawon watanni biyu.

Duk kayan da a saka da gora na bukatar matakai masu yawa.

Da farko, akwai bukatar a tafi daji don yanko gora. Gora na da nauyin, mai karfi na iya daukar uku ko hudu a baya, ga gajere kamar yadda Liu Xiabing take, tana shan wahala wajen dauke guda daya kawai.

Liu Xiabing ta ce, kayan aiki daban-daban suna bukatar zabar gora irin daban-daban. Ga misalin, gidan kyanwa na bukatar kayan aiki masu karfi, don haka dole ne a zabi gora mai shekaru hudu ko biyar, game da wadancan abubuwa kamar kwandunan 'ya'yan itace, gora mai shekaru uku ko hudu ne ake bukata shi ke nan.

Bayan an raba cikakken bututun gora, ana bukatar kara raba su zuwa sili daban-daban bisa kauri da fadi, ana gudanar da wadannan matakai masu wahala ne domin share fagen aikin saka da za a yi nan gaba. Alal misali, sakar wani kwandon 'ya'yan itace na bukatar nau'ikan sili guda 6. Saka gidan kyanwa ya samo asali ne a kan sakar kwandunan 'ya'yan itace, amma, bisa ga bukatun masu kiwon kyanwa, an kara karin mataki na samar da sauti. Kowace rana, a cikin ma'ajin gidan Liu Xiabing, akwai wasu 'yan'uwa mata dake zaune a kan kujera, suna saka wani gidan kyanwa akan cinyar su, hannayensu suna goge kan silin gora, hakan yana sa hannayen su kurjewa, sai dai daga baya su yanke wurin. Wani gidan kyanwa mai fadi santimita 40, yana bukatar kwararren ma'aikaci ya yi awa uku ko hudu don kammalawa, idan aka kara lokacin shiryawa, to za a yi amfani da awa kusan biyar domin kammala dukkan aikin.

Bayan an farfado da sakar dake amfani da gora ta Lingshan, masu saka da yawa sun koma garinsu na Pingnan, sun kama wannan tsohuwar sana’a ta gargajiya. Suna son irin wannan aiki, saboda ba za su bar gida ba, suna iya samun kudin shiga a yayin da suke kulawa da tsoffi da yara. Sannu a hankali, zaman rayuwar mazauna kauyen na samun kyautatuwa. Ya zuwa yanzu, iyalin Liu Xiabing ya jagoranci masu saka sama da 600 zuwa kara samun kudin shiga ta hanyar sayar da kayan da ake saka da gora, matasa da yawa ma sun soma koyon wannan fasahar gargajiya.

Kullum Liu Xiabing na ganin cewa, sana’ar saka da gora, wata sana’a ce mai fa’ida. Bayan gidan kyanwa da aka saka da gora ya samu karbuwa, sai ta ji cewa tana da sabon tunani kan makomar sana’arta a nan gaba.

Baya ga ci gaba da sayar da kayayyakin cinikayya na gargajiya da aka saka da gora, kuma tana tsayawa kan gidan kyanwa, don fitar da jerin wasu sabbin dabaru daya bayan daya game da kayan dabbobi. Ta tsara jakar kyanwa mai gida gida, da jakar kyanwa, da kuma wasu kayayyakin wasan kyanwa, wasu ma ta tsara ne bisa shawarar masu kallo yanar gizo.

Sana'ar saka da gora da kowane gida a garin Pingnan ke iya yi tana nuna wani sabon yanayi sakamakon saurin ci gaban yanar gizo, da kokarin matasan da suka dawo gida don fara sana'o'insu.

Bayan rana ta fadi, ko shakka babu za ta kara fitowa…..