logo

HAUSA

Xi ya jaddada kudurin ingiza kafuwar sabon salon ci gaba

2023-02-01 19:16:12 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya jaddada kudurin gwamnatin sa, na kara azamar ingiza kafuwar sabon salon ci gaba, da bunkasa tsaro da dabarun wanzar da ci gaba.

Shugaba Xi ya yi tsokacin ne da tsakar ranar jiya Talata, yayin da yake halartar taron karawa juna sani karo na 2, na hukumar siyasa ta JKS ta kwamitin koli na 20.  (Saminu Alhassan)