Bikin gargajiya na Sinawa na taka rawa sosai ga farfado da tattalin arzikin kasar Sin
2023-02-01 09:27:22 CMG Hausa
A karshen makon jiya ne miliyoyin al’ummar Sinawa suka koma bakin aiki, bayan kammalar hutun mako guda na bikin bazara, ko bikin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, bikin da shi ne mafi kasaita ga al’ummar kasar ta Sin.
A bana, bikin ya zo a gabar da gwamnatin kasar ta sassauta matakan kandagarki, da na yaki da annobar COVID-19, wadanda cikin shekaru 3 da suka gabata, suka haifar da takaita tafiye-tafiye, da sauran harkokin cudanyar al’umma.
Yayin bikin bazara na wannan karo, al’ummar kasar Sin sun samu zarafin haduwa da iyalai, da sada zumunta, da gudanar da tafiye-tafiye na yawon bude ido a cikin kasar da kuma ketare, wanda hakan ya yi matukar ingiza hada-hadar cinikayya, da bunkasa harkokin nishadantarwa.
A iya cewa, albarkacin bikin bazara na bana, kasar Sin ta kara farfado da hada-hadar cinikayya a gida, da bude kofofin cudanyar al’umma ta fannin yawon shakatawa zuwa kasashe makwaftanta, da ma na sauran sassan duniya. Kaza lika, yawan sayayyar da Sinawa suka yi yayin bikin na bazara ta karu matuka, idan an kwatanta da na makamancin lokaci a shekarar bara, wanda hakan ke nuna yadda bikin na sabuwar shekarar Zomo bisa kalandar gargajiya ta Sin, ya zamo wata alama dake haskaka ci gaban da Sin din ta samu a fannin farfadowa, da raya hada hadar tattalin arziki a gida, da ma tasirin hakan ga tattalin arzikin duniya baki daya. (Ibrahim Yaya, Saminu Hassan, Sanusi Chen)