logo

HAUSA

Wakilin Sin ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar ministan wajen Gabon

2023-02-01 21:16:37 CMG Hausa

Wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai lura da harkokin Afirka Liu Yuxi, ya ziyarci ofishin jakadancin kasar Gabon dake birnin Beijing a yau Laraba, inda ya gabatar da sakon ta’aziyyar rasuwar ministan wajen Gabon Michael Moussa Adamo.

Liu Yuxi, ya ce a madadin gwamnatin kasar Sin, yana mika sakon jajen rasuwar Moussa, yana kuma bayyana matukar alhinin sa ga iyalan mamacin.  (Saminu Alhassan)