logo

HAUSA

Najeriya za ta ci gaba da martaba yarjejeniyar zuba jari da kasashen Singaphore da Morocco da kuma Saudiya

2023-02-01 09:26:38 CMG Hausa

A ranar Talata 31 ga wata, ministan masana’antun tarayyar Najeriya Otunba Adeniyi Adebayo ya tabbatar da cewa, Najeriya za ta ci gaba da martaba yarjejeniyar zuba da kariya da ta kulla da kasashen Singapore da Morocco da kuma Saudiya.

Ministan ya tabbatar da hakan ne a birnin Abuja yayin taron manema labarai karo na 20 da ma’aikatar yada labarai ta shirya domin zayyana nasarorin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shi dai wanan taron manema labarai an fara gudanar da shi watanni biyu da suka gabata karkashin jagorancin ministan yada labarai na tarayyar Najeriya Lai Muhammad, inda ake baiwa ministocin ma’aikatu daban daban damar bayani dalla-dalla ga al’ummar kasa irin nasarorin da gwamnati ta samu a ma’aikatunsu a tsawon shekaru 8 na gwamnatin Buhari.

A yayin da yake gabatar da bayanansa, ministan ma’aikatar masana’antun Otumba Adeniyi ya ce, tun a ranar 16 ga watan Satumbar bara, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan yarjejeniyar inganta alaka ta kasuwanci da kuma kariya ga masu saka jarin na wadanann kasashen 3.

Yarjejeniyar ta kunshi yin sassauci kan kudin haraji da kuma samar da karin damarmakin da za su karfafa gwiwar masu saka jarin sha’awar fadada harkokinsu a kasar. 

Ministan ya sanar da cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya a tsakanin shekaru 8 na mulkin shugaba Muhammadu Buhari ta samu sama da dala biliyan 1 daga jarin da aka saka a bangaren masana’antar samar da motoci, kuma akwai alamu dake nuna kudin za su zarta haka da zarar an shiga mataki na gaba na harkokin samar da motocin.

“Wannan jari da dala biliyan guda da aka saka, an kiyasta kamfanin samar da mototcin zai iya kera mototci dubu 400 a shekara.”

Ya ce kuma ba da jimawa ba za a kammala cikakken kundin tsare-tsaren ci gaba na gwamnati a fagen sha’anin masana’antun samar da motoci. (Garba Abdullahi Bagwai)