logo

HAUSA

Yadda Sinawa ke yawon shakatawa a lokacin bikin bazara

2023-01-31 18:54:11 CMG Hausa

Yadda al’ummar Sinawa ke yawon shakatawa ke nan a sassa daban daban na kasar Sin, a yayin bikin bazara na wannan shekara, matakin da ya sa harkokin yawon shakatawa da suka samu koma baya a sakamakon annobar Covid-19 a cikin shekaru uku da suka wuce, suka farfado matuka a farkon wannan shekara. Alkaluman da aka samar sun yi nuni da cewa, yawan wadanda suka yi bulaguro a cikin kasar Sin, a lokacin hutun bikin na tsawon mako guda ya kai miliyan 308, adadin da ya karu da kashi 23.1% kan na bara. Kana yawan kudaden shiga da aka samu a fannin ya karu da kashi 30% kan na bara. (Lubabatu)