logo

HAUSA

CMG Ta Samu Lambar Yabo Ta Golden Ginnaree Awards Ta Thailand

2023-01-31 14:35:21 CMG Hausa

Kwanan baya, shirin telibijin na “ziyartar kasar Sin” ya samu lambar yabo ta “Golden Ginnaree Awards” ta kasar Thailand a karo na 8, shirin da cibiyar watsa shirye-shirye a yankunan Asiya da Afirka, na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG, da gidan telibijin na NATION na Thailand suka tsara cikin hadin gwiwa.

Lambar yabon “Golden Ginnaree Awards” tana daya daga cikin lambobin yabo mafiya tasiri a fannin shirye-shiryen telibijin na Thailand. Kuma a kan shirin “ziyartar kasar Sin” ne aka fara ba da lambar yabon ga shirin da kafofin yada labaru na kasashen waje suka tsara.

Mai gabatar da lambar yabon ya yi bayani da cewa, shirin na “ziyartar kasar Sin” ya bude idanun ’yan kallon Thailand dangane da kasar Sin.   (Tasallah Yuan)