logo

HAUSA

Kasashen Nijar, Kamaru da Chadi za su rinka amfani da tashar dakon kaya da aka bude a jihar Kano

2023-01-31 09:30:57 CMG Hausa

 

A ranar Litinin 30 ga wata, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci kaddamar da tashar fita da shigo da kaya daga waje ta tsandauri a jihar Kano dake arewacin Najeriya.

Tashar za ta baiwa ’yan kasuwa damar kawo kayansu daga ko ina a duniya kai tsaye zuwa Kano maimakon yadda a baya sai sun je bakin teku a jihar Legos sun dauko.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Tun a 2006 majalissar zartarwa ta tarayyar Najeriya ta amince da samar da tashar a wani mataki na kokarin rage cunkoso a tasoshin ruwan kasar, sannan kuma a rage wahalhalun da ’yan kasuwa ke fuskanta wajen  fitar da kaya da kuma shigo da su musamman ma wadanda jihohin suke nesa da bakin teku.

A lokacin da yake jawabi yayin bikin kaddamar da tashar, ministan sufuri na tarayyar Najeriya Alh Mu’azu Jaji Sambo ya ce, yanzu harkokin tattalin arzikin duniya yana tafiya ne cikin hanzari, a saboda haka gwamnatin tarayyar Najeriya ta ga dacewa kara tasoshin dakon kaya na tsandauri domin ya taimaka wajen hanzarta fitar da kayayyakin da ake samarwa a cikin gida da kuma shigo da su daga waje ba tare da daukar wani lokaci mai tsawo ba. 

Ministan ya ce, an yanke shawarar samar da tashar a jihar Kano ne saboda matsayinta na cibiyar kasuwanci a arewacin Najeriya, sannan kuma ta kasance jihar da aka fi hada-hadar kayan amfanin gona.

Alhaji Mu’azu Jaji Sambo ya ci gaba da cewar ’yan kasuwa dake kasashe makwafta kamar Nijar da Chadi da kuma Kamaru za su amfana sosai da wannan tasha wajen fitarwa da kuma shigo da kayayyaki zuwa kasashensu cikin sauki da kuma rangwamen kashe kudaden dako.

Da yake jawabi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, kaddamar da wannan tasha da ya yi a ranar ta Litinin 30 ta tabbatar da azamar da Najeriya ke da ita wajen cimma kudurin yarjejeniyar kwamatin hadakar ministocin Najeriya da Nijar na hukumar bunkasuwar tattalin arzikin kasashen biyu.

Shugaban Muhammadu Buhari ya yi fatan kasashe makwafta za su yi kokarin cin gajiyar wannan tasha domin bunkasar tattalin arzikinsu ta hanyar kulla alaka ta cinikayya tsakaninsu da ’yan kasuwar kasashen duniya.

Ya ci gaba da cewa, zaman lafiyar kowanne shugaba a duniya shi ne ya yi kokarin kyautata alakarsa da kasashen da suke makwaftaka da shi ta fuskokin tattalin arziki, tsaro da kuma diplomasiyya.

“Idan za ku iya tunawa lokacin da na zama shugaban kasa a zangon na farko, na ziyarci kasashen nan uku wato Nijar, Kamaru da Chadi, saboda kulla alaka ta mutuntaka tsakanin ka da makwafci da kuma a gwamatance abin bukata ne mutuka, domin muddin ba ka da wata alaka da kasashe to lallai kana cikin hatsari sosai domin kuwa za su iya haifar maka da gagarimar matsala ta fuskar tafiyar da gwamnatinka da kuma sha’anin tsaron kasarka. A don haka lallai wannan tasha babbar gada ce da za ta kara inganta mu’amulla mu da makwafta baya ga kyautata harkokin ’yan kasuwarmu masu sana’ar fito.”

Tsabar kudi dolar miliyan 27 aka kashe wajen gina tashar tsandaurin ta Dala dryport, yayin da kuma gwamnatin Kano ta kashe Naira biliyan 2.3 wajen gina tituna a cikin tashar a matsayin nata kason na hadin gwiwa wajen tafiyar da tashar. Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)