logo

HAUSA

Al’ummun jamhuriyar Nijar na kokarin bunkasa aikin noman rani da kiwo

2023-01-30 11:05:08 CRI

Kashi biyu cikin uku na fadin kasar Nijar ya zama shimfidar hamada da fari, amma duk haka, a Nijar noma da kiwo sun kasance muhimman ayyukan tun fil azal ga mutane. Fiye da kashi tamanin cikin dari na yankunan karkara, noma da kiwo suka fi rinjaye. Kuma amfanin noma na dadada raguwa ta illolin dalilin sauyin yanayi, sai dai domin cike gibin rashin damana mai kyau, yawancin mutanen karkara na aiki noman rani da aikin garake. Aka Rabo na daya daga cikin matan Dogondoutchi, yankin Dosso da ke kokarin maida hankali kan noman rani.

“Muna ta son shi domin muna ganin ana ta zuwa ga kayan noman rani, yanzu idan ka tashi ka tafi can kana iske noman rani na karfi muna yi, muna daukar ruwa kwakware muna ban ruwa da hannuwanmu salati yana nan mun sa. Mun gane amfanin noman rani, sai dai ba mu da ruwan da za mu yin shi, muna son shi kwarai."

Duk da cewa noman rauni na taimakawa wajen kara samun abinci, Malam Abdou Leko, magidanci kuma manomi, na ganin cewa talaka na dogaro ne da noma da kiwo.

"Idan ka duba rayuwar talaka aikin shi noma ne ko kiwo, kuma gwamnati duk irin nata kokari E… da za ta yi, za ta yi bisa kokarin kyautatawa talakawan kasa ne, su kuma talakawan nan idan aka duba aka gani minene aikinsu, minene sana’arsu a yanzu daga noman nan sai kiwo. Idan rani ya yi babu wata sana’a takamaimai wanda talaka ya rike babu shi. Kuma abin da ya noma din tana yiyuwa wata shekarar din a samu amfani, wata shekarar amfanin ya yi kadan. Kuma talakan dole sai ya ci abinci domin abinci shi ne na farko kan kowa. To yaya talaka zai yi, mutane wadanda suke cikin kauyuka da wadanda suke cikin ciyawa suna noma."

Sai dama, da shugaban kungiyar makiyaya, da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa idan ana son kyautatuwar noma da kiwo dole sai an karfafa zaman jituwa tsakanin manoma da makiyayi.

"Kiran da nike wa bangarori biyu na al’umma, da noma da kiwo dan inna ne da dan abba, kuma wanda ya ce ya shiga tsakaninsu ya zama shedan."

Ganin yadda jamhuriyar Nijar ke fama da kissar damana a kai a kai, ya zama wajibi ga gwamnati na ta kara zuba jari ta yadda ’yan kasa za su dukufa ga noma da kiwo.

Maman Ada, sashen hausa na CRI daga birnin Yamai a jamhuriyar Nijar. (Maman Ada)