logo

HAUSA

Wannan sabuwar tashar jirgin ruwa ta shaida wani tunani mai muhimmanci

2023-01-30 19:41:27 CMG Hausa

A makon da ya gabata, yayin da Sinawa suke murnar bikin sabuwar shekara ta gargajiya, an ji wani albishir daga Najeriya, wato an kaddamar da tashar jirgin ruwa ta Lekki a jihar Lagos, a ranar 23 ga watan Janairun bana.

Na tuna da lokacin da nake aiki a Najeriya a shekarar 2008, ana kokarin gina yankin ciniki mai ‘yanci na Lekki, wanda kamfanonin kasar Sin suka zuba jari a ciki. A lokacin, wasu abokaina Sinawa sun gaya mana cewa, nan gaba za a gina wata babbar tashar jirgin ruwa a kudancin yankin ciniki mai ‘yancin, wadda za ta taimakawa raya masana’antu da aikin fitar da kayayyaki zuwa ketare a cikin yankin. To, ga shi, yanzu an riga an cimma burin da aka sanya. Ta haka za mu iya ganin yadda kasar Najeriya take kokarin neman samun hakikanin ci gaba, duk da matsalolin da take fuskanta a fannonin tattalin arziki da tsaro, cikin wadannan shekarun da suka gabata.

Wannan sabuwar tashar jirgin ruwa dake Lekki ta burge ni a fannoni daban daban.

Da farko, wata ingantacciyar tasha ce da ake samun ruwa mai zurfi. Da ma na taba ganin wasu manyan jiragen ruwa masu daukar kaya, da suka tsaya a tashar jirgin ruwa dake Apapa da Tin Can Island, duk a jihar Lagos. Sai dai girman jirgin ruwan da tashar Lekki za ta iya dauka, ya ninka na wadancan jiragen ruwa har sau 4, wanda ya wuce na jirgin ruwa mafi girma da ake samu yanzu a duniyarmu. Ban da wannan kuma, wannan tashar jirgin ruwa za ta iya karbar kwantaina miliyan 1.2 a duk shekara, wanda yake kan gaba cikin dukkan tashoshin jirgin ruwa dake yammacin Afirka.

Na biyu, wannan sabuwar tasha za ta haifar da dimbin alfanu. A cewar gwamnan jihar Lagos ta Najeriya, Babajide Sanwo-Olu, wannan sabuwar tasha za ta sanya Lagos zama cibiyar jigilar kayayyaki ta hanyar teku dake tsakiya da yammacin Afirka, da samarwa Najeriya da guraben aikin yi da yawansu ya kai kusan dubu 200, inda ta haka za a samar da kyakkyawar damar raya tattalin arzikin kasar.

Sa’an nan na uku shi ne, dukkan ayyukan da suka shafi zuba jari, da ginawa, da ba da kulawa, masu alaka da wannan tasha, ana gudanar da su ne ta hanyar hadin gwiwar bangarorin kasashe daban daban. Inda kamfanonin kasar Sin, da na kasar Singapore, da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, da gwamnatin jihar Lagos suka zuba jari tare, sa’an nan wani kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin gina tasha, daga baya kuma, aka ba wani kamfanin kasar Faransa ragamar kulawa da gudanar da harkokin tashar. Wannan tsarin da ake bi ya nuna manufar sanya kowa ya shiga a dama da shi, da aiwatar da aiki ba tare da rufa-rufa ba, da ginawa gami da cin moriyar tashar tare.

Ban da wannan kuma, a matsayi na na wani Basine, ni ma ina alfahari da wannan sabuwar tashar jirgin ruwa.

Saboda wani kamfanin kasar Sin ya taka muhimmiyar rawa wajen aikin gina wannan tasha. Inda a cikin dalar Amurka biliyan 1.044 da aka zuba cikin tashar, kudin da wannan kamfanin kasar Sin ya zuba ya kai dala miliyan 221. Haka kuma, an fara aikin gina tashar a watan Yunin shekarar 2020, da kammala aikin a watan Oktoban shekarar 2022, daga baya an kaddamar da ita a farkon shekarar 2023, wanda ya zama watanni 2 kafin lokacin da aka tsara. Da ma mutane da yawa sun damu kan cewar watakila ba za a iya kammala aikin gini cikin lokaci ba, sakamakon annobar COVID-19 dake yaduwa a sassa daban daban. Amma wannan kamfanin kasar Sin da ya dauki nauyin gina tashar ya cika alkawarin da ya dauka, abun da ya nuna yadda yake da sahihanci da kwarewar aiki.

Ban da haka, ya kamata mu lura da cewa, dalilin da ya sa wannan kamfanin Sin zuba jari, da samar da fasahohi, da tura ma’aikatansa zuwa wajen gina tashar, shi ne domin shawarar hadin gwiwa ta “Ziri Daya da Hanya Daya” (B&R) da kasar Sin ta gabatar, gami da tunani na cin moriya tare gami da samun ci gaba tare da ya zama tubalin shawarar.

Wannan tunani ya tabbatar da aikace-aikacen kasar Sin, inda maimakon ta zama wata “shugaba” ko kuma “mai ba da sadaka” ga kasashen Afirka, take kokarin shiga aikin raya kasashen bisa matsayinta na wata abokiya dake son gudanar da takamaiman ayyukan hadin gwiwa. Kana yayin da ake gudanar da hadin gwiwar, kasar Sin ta tsaya kan manufar tattaunawa, da cin moriya tare, da gudanar da aiki tare, da girmama ka’idojin kasuwanci da na kasa da kasa, da lura da moriyar bangarori daban daban da damuwarsu, ta yadda take samarwa kasashen Afirka da hakikanin ci gaba.

Idan ana son tabbatar da sahihancin Sinawa yayin da ake hadin gwiwa da su, to, wannan sabuwar tashar jirgin ruwa dake Lekki shaida ce. (Bello Wang)