logo

HAUSA

Kasar Sin za ta samar da karfin farfado da tattalin arzikin duniya a shekarar 2023

2023-01-29 21:50:51 CMG Hausa

Rahoton da MDD ta fitar a kwanan baya, ya yi hasashen cewa, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin za ta karu zuwa kaso 4.8% a shekarar 2023, lamarin da zai sa ta zama jagoran bunkasuwar tattalin arzikin shiyyar da kasar Sin take. Ita ma a nata bangare, babbar daraktar kungiyar cinikayya ta duniya WTO madam Ngozi Okonjo-Iweala, a yayin da ta zanta da wakilinmu a kwanan baya, bayan da aka rufe taron dandalin tattalin arzikin duniya a garin Davos na kasar Switzerland, ta ce kasancewarta injin bunkasuwar tattalin arzikin duniya, yadda kasar Sin ta sake bude kofarta ga duniya, mataki ne da zai taimakawa duniya baki daya.

A hakika, bikin bazara da aka gudanar a kasar Sin a makon da ya gabata ya shaida hasashen da aka yi. Bikin bazara biki ne da al’ummar Sinawa ke yi na murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta wata, kuma bikin na bana ya kasance na farko da aka yi tun bayan da aka sassauta matakan kandagarkin cutar Covid-19, kuma sakamakon nasarorin da aka cimma cikin shekaru uku da suka wuce ta fannin dakile cutar, a bana, al’ummar Sinawa sun fi gudanar da bikin cikin murna da farin ciki, inda aka ga Sinawa masu yawan gaske na zuwa wuraren shakatawa, da gidajen sinima, da gidajen cin abin da sauransu.

Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, yawan wadanda suka yi bulaguro a cikin kasar Sin, a lokacin hutun bikin na tsawon mako guda ya kai miliyan 308, adadin da ya karu da kashi 23.1% kan na bara. Kana yawan kudaden shiga da aka samu a fannin ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 375.8, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 55.52, wanda ya karu da kashi 30% kan na bara. Sa’an nan kuma yawan kudaden tikitin kallon fina-finai a lokacin hutun ya kai yuan biliyan 6.758, wanda ya karu da kaso 11.89 kan na bara. Lallai duk wadannan sun sake shaidawa duniya babbar kasuwar kasar da kuma ingancin tattalin arzikin kasar.

A sa’i daya kuma, bayan da kasar Sin ta sassauta matakan kandagarkin cutar, da kuma maido da bulaguron da ’yan kasar ke yi zuwa ketare, Sinawa da yawa sun kuma tafi yawon shakatawa a kasashen ketare a yayin bikin na bana, kuma alkaluman da aka samar sun shaida cewa, yawan yarjejeniyoyin yawon shakatawa da baki Sinawa suka yi zuwa waje, a bana ya karu da kimanin kaso 640%.

A jajebirin bikin, rukunin baki masu yawon shakatawa na kasar Sin na farko tun bayan da aka sassauta matakan yaki da cutar ya sauka a birnin Alkahira, kuma sassan kula da harkokin yawon shakatawa da kayayyakin tarihi na kasar Masar sun shirya bikin maraba da dawowar bakin a filin jirgin sama. Haka ma lamarin yake a kasashen Switzerland, da Indonesia, da Maldive, da New Zealand da Turkiyya, wadanda suka yi suna ta fannin harkokin yawon shakatawa.

Kafofin yada labarai da suka hada da Prensa Latina, da Reuters, da kuma Itar-Tass, sun ba da rahotannin cewa, dawowar baki masu yawon shakatawa daga kasar Sin, za ta taimaka ga farfadowar harkokin yawon shakatawa a duniya baki daya.

Ana fatan alheri ga wannan sabuwar shekarar da aka shiga, kuma tabbas kasar Sin za ta samar da karfin farfado da tattalin arzikin duniya a wannan shekara. (Lubabatu Lei)