logo

HAUSA

Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya za ta gudanar da gwaji na tantance masu zabe

2023-01-28 10:20:11 CRI

A ranar 27 ga wata ne shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu ya gudanar da taro da daukacin kwamashinonin zaben jahohi a hedikwatar hukumar dake birnin Abuja, a daidai lokacin da ya rage kasa da kwanaki 28 a gudanar da zaben shugaban kasa da na ’yan majalissar dokoki .

A yayin taron shugaban hukumar zaben, ya ce, hukumarsa ba za ta taba bari duk wani dan kasa da ya isa yin zabe a bar shi a baya ba, ba tare da ya samu damar gudanar da zabe ba.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Farfesaa Mahmud Yakubu ya ce, za a gudanar da gwaji na aikin tantance masu zaben ne a ranar 4 ga watan gobe, kuma za a gudanar da wannan aiki ne a akwatinan zabe 436 dake sassa daban-daban na kasar.

Ya ci gaba da cewa, kowacce jiha an zabi akwatina guda 12 da za a gudaar da wannan gwaji yayin da birnin Abuja kuma aka zabi akwatina guda 4 duk don tabbatar da ganin an yi raba daidai a tsakanin gundumomin ’yan majalissar dattawa 109 da ake da su a tarayyar Najeriyar.

Ya ce hukumar dai ta dauki wannan mataki ne domin kara tabbatarwa ’yan Najeriya irin shirin da ta yi da kuma sahihancin na’urorin zaben da ta yi wo oda.

“Yanzu haka an kammala kai kayayyakin zabe da ba su da hatsari sosai zuwa sassa daban daban na kasar nan, kuma nan gaba kadan za a fara bayar da horo ga jami’an zabe yayin da kuma za mu kara matsa kaimi wajen tuntubar masu ruwa da tsaki kan harkar zabe.

“Mun kuma yi nisa wajen jigilar mahimman kayan zabe da suke matukar bukatar tsaro zuwa jahohi ta amfani da jiragen sama, yayin da kuma mun kammala tantance masu sanya ido na gida da na kasashen waje kana da wakilan kafofin yada labarai.”

Shugaban hukumar zaben a tarayyar Najeriya ya kara tabbatar da cewa, masu ababen hawa da hukumar za ta yi amfani da su wajen zurgar-zurgar ma’aikatan zabe da kayansu sun bada tabbacin aiki tukuru, yayin da su ma jami’an tsaro sun tabbatarwa hukumar ci gaba da bada hadin kansu wajen samar da tsaro a kowanne sashe na kasar.

A yayin taron dukkannin kwamashinonin zaben na jahohi sun yi bayani yanayin da ake ciki a jahohinsu kan batun rabon katin zabe na din-din-din, inda hukumar zaben ta kara jaddada kira ga dukkanin wani dan Najeriya da bai karbi katinsa ba ya hanzarta domin sauke nauyin kasa dake wuyansa yayin zabukan dake tafe. (Garba Abdullahi Bagwai)