logo

HAUSA

Amurka: yawan wadanda aka kwantar a asibiti sakamakon kamuwa da cutar influenza ya kafa tarihi a shekaru fiye da goma

2023-01-28 15:26:33 CMG Hausa

Alkaluman da cibiyar dakile da kandagarkin cututtuka ta kasar Amurka ta kaddamar a kwanan baya sun nuna cewa, a shekarar 2022 yawan masu fama da cutar influenza ko mura ya ci gaba da karuwa. An kiyasta cewa, a kalla mutane fiye da miliyan 1 da dubu 600 ne suka kamu da cutar ta influenza, ciki hadda wasu dubu 13 da aka kwantar a asibiti, yayin da wasu 730 kuma suka rasa rayukansu.

Alkaluman cibiyar dakile da kandagarkin cututtuka ta kasar Amurka sun nuna cewa, yawan masu kamuwa da cutar ta influenza ya fi yawa a kudu maso gabashin da kuma kudu maso tsakiyar kasar ta Amurka. Yanzu yawan wadanda aka kwantar a asibiti sakamakon kamuwa da cutar influenza, ya kafa tarihi bisa makamancin lokaci tun bayan shekarar 2010.

Rahotanni a shafin internet na cibiyar cibiyar dakile da kandagarkin cututtuka ta kasar Amurka na cewa, a kan samu masu kamuwa da cutar da dama a lokacin kaka da na hunturu a kasar, wato daga watan Disamba zuwa watan Febrairu na shekara mai kamawa. A shekarar 2022, cutar influenza ta barke kafin lokacin da aka saba, don haka an samu karuwar masu kamuwa da cutar kafin lokacin da aka saba, a ciki har da kananan yara da tsoffafi masu dimbin yawa.

Bayan ga yaduwar cutar ta influenza, yawan masu kamuwa da sauran cututtukan da suka shafi sassan jiki masu taimakawa numfashi, shi ma ya ci gaba da karuwa a kasar Amurka. A wasu sassan kasar, yawan kananan yara masu fama da cututtukan da suka shafi sassan jiki masu taimakawa numfashi, ya karu sosai cikin gajeren lokaci, har ma babu isassun gadaje a wasu asibitocin. Masana sun yi gargadin cewa, a yanzu da aka shiga lokacin hunturu a kasar Amurka, Amurkawa suna fuskantar annobar cutar COVID-19, cutar influenza da cutar RSV da ta shafi sassan jiki masu taimakawa numfashi dukka.

To, ta yaya za a kare mutane daga kamuwa da cutar influenza? Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan dake Beijing ta yi bayani da cewa, yin allurar rigakafin cutar influenza a ko wace shekara, ita ce hanya mafi dacewa wajen yaki da cutar. Yin allurar ba kawai yana kare mutane daga kamuwa da cutar ba, har ma yana kiyaye mutane daga fadawa cikin matsananin hali. Don haka, ya dace a rika yiwa jarirai ‘yan sama da watanni 6 a duniya alluran a ko wace shekara. (Tasallah Yuan)