logo

HAUSA

Bikin Bazara Na Gargajiyar Kasar Sin Ya Kara Azama Kan Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya

2023-01-28 21:31:05 CMG HAUSA

Kwanan baya, mahukuntan kasar Sin sun gabatar da alkaluman tattalin arziki dangane da lokacin hutun bikin Bazara na gargajiyar kasar Sin na bana. Yawan wadanda suka yi bulaguro a cikin gidan kasar Sin ya kai miliyan 308, wanda ya karu da kashi 23.1 bisa dari kan na bara. Kana yawan kudaden shiga da aka samu a fannin yawon bude ido a cikin gida a lokacin hutun na tsawon mako guda, ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 375.8, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 55.52, wanda ya karu da kashi 30 cikin dari kan na bara. Sa’an nan kuma yawan kudaden tikitin kallon fina-finai a lokacin hutun ya kai yuan biliyan 6.758, wanda ya karu da kaso 11.89 kan bara. Yawan wadanda suka shiga kasar Sin daga ketare da zuwa ketare daga kasar Sin kuma ya karu da kaso 120.5 kan shekarar 2022.

Bikin Bazara na bana, shi ne irinsa na farko, tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da sabbin matakin yaki da cutar COVID-19. Zirga-zirgar mutane sun samu farfadowa cikin sauri a kasar Sin. Alkaluman sun nuna kuzarin kasar Sin na yin sayayya.

Haka zalika an samu karin mutane da suka yi murnar bikin Bazara a ketare. Alkaluma sun nuna cewa, kwagilolin da mutanen Sin suka daddale kan yin bulaguro a ketare a lokacin hutun bikin Bazara a bana ya karu da kaso 640 bisa na shekarar bara. A rana ta farko ta shekarar Zomo kuma, an shirya kasaitaccen bikin maraba da jirgin sama na farko a bana dake dauke da masu yawon shakatawa na kasar Sin a tsibitin Bali na kasar Indonesia, lamarin da kafofin yada labaru da dama suka watsa labaru a kai. Wasu kafofin yada labaru na kasashen waje sun yi nuni da cewa, miliyoyin masu yawon shakatawa na kasar Sin za su kara azama kan farfadowar otel-otel, aikin yawon shakatawa da kasuwanci na duniya.

Yanzu haka ana fuskantar sauye-sauye a duniya. Kasar Sin ba ta aza harsashi sosai wajen farfado da tattalin arziki ba. Tana bukatar kara yin kokarin farfado da tattalin arzikinta. Amma al’ummar Sin na da imani da kuma kwarewa wajen farfado da tattalin arzikin kasar a shekarar 2023 da ake ciki. (Tasallah Yuan)