logo

HAUSA

Mutanen da suka mutu sakamakon tashin Bom a jihar Nasarawa sun kai 40

2023-01-27 15:50:52 CMG Hausa

A ranar Alhamis 26 ga wata gwamnatin jihar Nasarawa dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta tabbatar da cewa, mutane 40 ne suka mutu sakamakon tashin wani bom a kauyen Rukubi dake kan iyakar jihar da jihar Benue.

Gwamnan jihar Alhaji Abdullahi Sule ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Lafiya, fadar gwamnatin jihar.

 

A yanzu haka dai gwamnati ta kafa kwamati da zai bibiyi musabbabin tashin wannan Bom.

Gwamna Abdulahi Sule wanda ya jajantawa iyalai da ’yan uwan wadanda suka rasa rayukansu sakamkon wannan al’amari, ya kuma yi kira ga al’umomin yankin da su kwantar da hankulansu, gwamnati za ta yi bakin kokarinta domin gudanar da cikakken bincike da nufin gano wadanda suke da hannu a tashin bom din.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, tuni aka aike da jami’an tsaro zuwa yankin karamar hukumar Doma domin kwantar da hankulan al’ummar yankin, inda ya bukaci jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Daga tarayyar Najeriya, Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)