logo

HAUSA

Al’adar Sinawa ta kirga shekaru da dabbobi

2023-01-27 17:44:36 CRI

Yanzu haka al’ummar Sinawa na shagulgulan bikin bazara, bikin da ya kasance mai muhimmanci kuma mafi kasaita a gare su. Kamar yadda muka bayyana a shirin mu na baya, bikin bazara biki ne da ke alamanta shiga wata sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar Sinawa, amma ko kun san wannan sabuwar shekara da za a shiga Sinawa suna kuma kiranta shekarar Zomo? Mene ne dalilin hakan?

Lallai, dalili shi ne Sinawa na da wata al’adar gargajiya ta kirga shekaru da dabbobi, kuma dabbobi 12 ne ake amfani da su, wato Bera, da Saniya, da Damisa, da Zomo, da Dragon, da Maciji, da Doki, da Tunkiya, da Biri, da Kaza, da Kare da kuma Alade, kuma ana zagaya duk dabbobin a shekaru 12.

A kasance tare da mu cikin shirin, don jin karin haske.(Lubabatu)