Shugaba Xi ya taya Bob Dadae murnar sake lashe zaben jagorancin Papua New Guinea
2023-01-27 21:18:11 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga Mr. Bob Dadae, bisa sake lashe zaben babban gwamnan Papua New Guinea ko PNG.
Cikin sakon na sa, Xi ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da Dadae, wajen fadada nasarorin da aka cimma a baya, da kuma dorawa daga inda aka tsaya bisa tsanaki, da wanzar da ci gaban dangantakar sassan biyu. (Saminu Alhassan)