logo

HAUSA

Amurka ta bayyana cimma nasarar hallaka babban jagoran ISIS a Somalia

2023-01-27 16:55:26 CMG Hausa

Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya ce wasu hare haren soji da dakarun Amurka suka kaddamar a Somaliya, sun hallaka mayakan kungiyar ISIS, ciki har da wani babban kusanta.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis, Mr. Austin ya ce sojojin Amurka sun kaddamar da hare haren ne a ranar Laraba, kuma cikin mayakan ISIS din da suka kwanta dama har da Bilal-al-Sudani, jigo a kungiyar, kuma jagoran yada da’awar kungiyar a sassa daban daban na duniya.

Sanarwar ta ce Al-Sudani ne ke ingiza yaduwar kungiyar ISIS a sassan nahiyar Afirka, tare da samar da kudaden aiwatar da ayyukan kungiyar a sassan duniya ciki har da kasar Afghanistan.

Bayan samun umarni daga shugaba Joe Biden, dakarun sojin Amurka sun kaddamar da hare hare a arewacin Somalia, kuma ayyukan sojin ba su rika da fararen hula ba.  (Saminu Alhassan)