logo

HAUSA

Matakan yaki da COVID-19 na Sin za su taimaka wajen dawo da tsarin samar da hajoji, in ji wani masani

2023-01-27 16:43:04 CMG Hausa

Matakan yaki da COVID-19 na Sin za su taimaka wajen dawo da tsarin samar da hajoji, in ji wani masani

Masani a fannin harkokin kudi a kasar Ghana Alex Ampaabeng, ya ce matakin da Sin ta dauka na dage tsauraran matakan yaki da annobar COVID-19, zai taimaka wajen farfado da tsarin samar da hajoji na duniya.

Alex Ampaabeng, wanda ke aiki da kwamitin shawo kan fari a Ghana, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan nan cewa, matakan inganta yaki da annobar COVID-19 da Sin ke aiwatarwa a yanzu, sun samu karbuwa, kasancewar za su bunkasa tattalin arzikin duniya, tare da ingiza yawan cinikayyar kasa da kasa tsakanin kasar da sauran sassan duniya.

Masananin ya kara da cewa, kasar Sin ita ce ta biyu a duniya a fannin karfin tattalin arziki. Kuma Ghana da kasashe da dama, na gudanar da cinikayya mai tarin yawa tare da Sin. Don haka bayan sake bude kofofin ta ga duniya don farfado da al’amura, hauhawar farashi sakamakon karancin hajoji zai yi sauki kwarai.

Yayin mako guda na hutun bikin bazara, sassan nishadantarwa, kamar Sinima da wuraren bude ido a kasar Sin sun cika da jama’a, kuma a cewar Ampaabeng, tafiye tafiye, da sayayya da Sinawa suka yi yayin wannan lokaci na bikin bazara, na nuni ga karsashin tattalin arzikin kasar Sin, wanda zai kara bunkasa kwarin gwiwar jama’a a fannin dawowar hada hadar tattalin arziki a kasar.

Ampaabeng, ya kara da cewa, Sin na daya daga manyan abokan huldar cinikayya da kasar Ghana, kuma Ghana za ta ci gaba da samun karin kudaden shiga, ta fannin haraji da za a tara, sakamakon matakin da Sin ta dauka na dage tsauraran matakan yaki da annobar COVID-19. (Saminu Alhassan)