logo

HAUSA

Bayan tafiye-tafiyen sabuwar shekara adadin harbuwa da cutar COVID-19 a sassan Afirka ya yi kasa da na shekarun baya

2023-01-27 16:53:45 CMG Hausa

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta ce adadin wadanda suka harbu da cutar COVID-19 yayin tafiye tafiyen bukukuwan sabuwar shekara a sassan nahiyar Afirka ya ragu matuka, idan an kwatanta da adadin da aka samu a shekarun baya bayan nan.

Wata sanarwa da WHO ta fitar a jiya Alhamis, ta ce cikin makwanni 3 na farkon watan Janairun nan, adadin sabbin masu harbuwa da cutar bai wuce 20,552 ba, adadin da ya ragu da kaso 97 bisa dari, idan an kwatanta da na makamancin lokacin shekarar bara, duk da karuwar masu kamuwa da cutar da aka samu a kasashen Afirka ta kudu, da Tunisia, da Zambia, cikin makwanni 2 da suka gabata.

Ana dai ganin mai yiwuwa raguwar alkaluman na da nasaba da rashin yin gwajin cutar, amma duk da haka, adadin wadanda ake kwantarwa a asibiti, da wadanda cutar ke hallakawa sun yi matukar raguwa. Ya zuwa ranar 22 ga watan nan, mutane 88 ne aka tabbatar sun rasu sakamakon cutar ta COVID-19, adadin da ya yi kasa da wanda aka samu a shekarar 2022, wanda ya kai mutum 9,096.

To sai dai a cewar daraktar shiyyar Afirka a WHO Matshidiso Moeti, ana ci gaba da samun yaduwar nau’o’in cutar, kuma yana da muhimmanci ga kasashen nahiyar su kasance cikin shirin ko ta kwana, domin gaggauta ganowa da kuma dakile saurin bazuwar cutar.   (Saminu Alhassan)