logo

HAUSA

Zargin “Tarkon Bashi” na shan suka daga sassan Afirka

2023-01-26 19:49:00 CMG Hausa

Ga duk mai bibiyar kafafen watsa labaran yammacin duniya, da irin kalaman da kan fito daga bakunan manyan jami’an Amurka, ba zai rasa jin zarge-zarge marasa dalili kan kasar Sin ba. Cikin wadanda suka fi fitowa fili, a baya bayan nan an ji zargin cewa wai kasar Sin na “Danawa kasashen Afirka Tarkon Bashi”. Kana a baya bayan nan ma, an jiyo sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen, na cewa wai Sin ta yiwa shirin tattaunawa game da lamunin da kasar Zambia ke karba kafar ungulu.

Idan muka bibiyi wannan kalamai na Janet Yellen, za mu ga ba su da tushe ko kadan, domin kuma su kansu mahukuntan kasar Zambia sun musanta hakan, suna masu bayyana kalaman da cewa sam ba su dace su fito daga bakin babbar jami’ar Amurka ba. Har ma wasu masu fashin baki na cewa bai dace jami’ar ta furta kalamai masu nasaba da alakar Sin da Zambia, yayin da take ziyarar aiki a Zambia ba, domin da farko ma hakan ya sabawa da’ar ayyukan diflomasiyya.

Kaza lika, matsayar Sin game da bashin dake tsakaninta da Zambia a bayyane take, kasancewar Sin da Zambia kawaye ne na tsawon lokaci, kuma abokan hadin gwiwar samar da ci gaba. Ana iya shaida hakan, idan aka dubi yadda Sin ta tallafawa Zambia da kudaden gudanar da layin dogo da ya hada Tanzania da Zambia tun a shekarun 1970, lokacin da ita kanta Sin ba ta da cikakkiyar wadata.

Har ila yau a yanzu ma, Sin ta samar da kudaden aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a Zambia, wanda hakan ke dada tabbatar da aniyarta ta ingiza ci gaban kasar.

Ko shakka babu, kalaman waccan jami’a ta Amurka sun sabawa ka’ida, kuma akwai bukatar tsagin Amurka ya yi amfani da damarsa, ta inganta alaka da Zambia wajen gabatar da agaji na kara bunkasa kasar, maimakon mayar da Sin abun suka a idon sahihan kawayen ta na nahiyar Afirka.

Wasu dai na kallon irin wadannan kalamai daga jami’an Amurka, a matsayin kunna wutar yakin cacar baka, da nuna alamu na wata mummunar takara tsakanin ta da sauran kasashen duniya dake kawance da kasashen Afirka. Har ma wasu na cewa, idan har Amurka ba ta sauya matsa wajen kallon Sin a matsayin wata barazana ba, hakan na iya zama manuniya dake tabbatar da cewa, burin Amurka shi ne mayar da nahiyar Afirka fagen dagar takara, maimakon wuri da za a tallafawa ya samu ci gaban da yake fata, kuma nahiya da ke bukatar hadin kan dukkanin kasashen da suka ci gaba, ta yadda za a gudu tare a tsira tare! (Saminu Hassan)