logo

HAUSA

Kaso mai tsoka na ra’ayoyin jama’a ya nuna gamsuwa da nasarar kasar Sin a fannin kandagarkin COVID-19

2023-01-26 17:00:20 CMG Hausa

Sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a na kasa da kasa, wanda rukunin kwararru na kafar CGTN, da hadin gwiwar cibiyar nazarin ra’ayoyin jama’a ta jami’ar Renmin dake kasar Sin suka shirya sun nuna cewa, a kasashe 21 da suka hada da Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Jamus da Italiya, kaso 88.1 bisa dari na jama’a sun gamsu da matakan da kasar Sin ta aiwatar, a fannin kandagarki da shawo kan annobar COVID-19 cikin shekaru 3 da suka gabata, adadin da kuma ya kai kaso 93.4 bisa dari a tsakanin jama’ar nahiyar Asiya, da kasashen Afirka da na Latin Amurka.

Game da shirin Sin na rage matsin matakan dakile yaduwar annobar kuwa, daga matsayin A zuwa B, kaso 76.2 bisa dari na wadanda aka ji ra’ayoyin su sun gamsu da tasirin hakan. Kuma wannan adadi ya ma haura tsakanin al’ummun Asiya, da Afirka da Latin Amurka zuwa kaso 82.5 bisa dari.

Cikin shekaru 3 da suka gabata, kasar Sin ta samar da alluran rigakafin COVID-19 sama da biliyan 2.2, ga sama da kasashe da hukumomin kasa da kasa 120. Kaza lika Sin ta samar da tallafin kayan kariyar jiki, da na’urorin samar da iskar shaka, da takunkumin baki da hanci, da sauran kayayyakin da ake bukata na yaki da annobar ga kasashe 153, da hukumomin kasa da kasa 15.

Kuri’un jin ra’ayin jama’ar ya kuma nuna kaso sama da 85 bisa dari na wadanda aka ji ta bakin su, sun gamsu da gudummawar kasar Sin a fannin yaki da COVID-19 a matakin kasa da kasa.

A Najeriya da Pakistan, inda Sin ta aike da tallafin alluran rigakafin cutar, kaso 88 bisa dari na masu bayyana ra’ayin, sun amince da ingancin alluran na kasar Sin.  (Saminu Alhassan)