logo

HAUSA

Wakilin Sin ya tabbatar da muhimmancin aiwatar da matakan dagewa Sudan takunkumai

2023-01-26 17:03:04 CMG Hausa

Mashawarci a ofishin wakilcin dindindin na Sin a MDD Liang Hengzhu, ya yi kira ga sassan kasa da kasa, da su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da an dagewa kasar Sudan takunkuman da aka kakaba mata. Liang wanda ya yi kiran a gaban mahalarta taron kwamitin tsaron MDD na jiya Laraba, ya ce sake gina tsarin bin doka, da tabbatar da adalaci a yankin Darfur na Sudan, burika ne na gamayyar kasashen duniya.

Jami’in ya kara da cewa, aiwatar da yarjejeniyar Juba, da tabbatar da ikon gwamnatin Sudan na wanzar da tsarin shari’a mai nagarta, na bukatar tallafin kudade. Don haka ya wajaba, sassan kasa da kasa su kaucewa siyasantar da batun Sudan, su tallafawa kasar, tare da aiwatar da dukkanin matakan da za su kai ga dagewa kasar takunkumai, da sauran batutuwa dake addabar kasar.

Daga nan sai jami’in ya sake jaddada cewa, matsayar kasar Sin game da shigar kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa cikin batun kasar Sudan ba ta sauyawa. Ya ce, "Muna fatan wannan kotu za ta nacewa ka’idojin lura da matsayar ta, da martaba ‘yancin Sudan na samun adalci a mataki na shari’a”. (Saminu Alhassan)