logo

HAUSA

Xi Jinping ya gabatar da sakon bidiyo ga taron koli karo na 7 na kungiyar kasashen Latin Amurka da Caribbean

2023-01-25 15:10:05 CMG Hausa

A jiya Talata 24 ga watan nan ne aka gudanar da taron koli na bakwai, na kungiyar kasashen Latin Amurka da Caribbean, a birnin Buenos Aires, fadar mulkin kasar Argentina. Bisa goron gayyatar da shugaban kasar Argentina, kuma mai rike da shugabancin kungiyar a wannan karo Alberto Fernández ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ta bidiyo a gun taron.

Cikin jawabin na sa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasashen yankin Latin Amurka da Caribbean, na kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin, don inganta raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” mai inganci, da ba da goyon baya da shiga ayyukan shawarar ci gaban duniya, da ta kiyaye tsaron duniya.

Baya ga haka, Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin yanzu, duniya ta shiga wani sabon yanayi na tinkarar tashin hankali da sauye-sauye, kuma ta hanyar karfafa hadin kai ne kadai za a iya tinkarar kalubale, tare da shawo kan matsaloli tare. Ya kara da cewa, kasarsa tana son yin aiki tare da kasashen Latin Amurka da Caribbean, don ci gaba da inganta zaman lafiya da bunkasuwar duniya, da sa kaimi ga gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil'adama, da samar da makoma mai kyau tare. (Mai fassara: Bilkisu Xin)