Al’ummun Sinawa na haduwar iyali, na murnar bikin bazara
2023-01-25 08:51:47 CMG Hausa
Bikin bazara wato Spring Festival a Turance, bikin gargajiya ne mafi kasaita ga Sinawa, da ke alamanta shiga sabuwar shekara bisa kalandar wata ta gargajiya ta kasar. Bikin bazara na kasar Sin yana da tsawon tarihin da ya kai kimanin shekaru 4000, kuma ya yi daidai da muhimmancin bikin Kirismeti ga Turawa, shi ne kuma biki mafi muhimmanci ga Sinawa.
Bikin a wannan shekara ya fado a ranar 21 ga watan Janairun 2023. Bikin Bazara na zuwa lokacin da Sinawa ke ban kwana da tsohuwar shekara, tare kuma da shiga cikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar. Sin kasa ce da ke mai da hankali kan aikin gona, a shekaru aru aru da suka gabata, ana amfani da taurari domin kokarin gudanar da harkokin aikin gona kamar yadda ake fata. Sakamakon haka, aka kirkiro kalandar wata a nan kasar Sin bisa tsarin tafiye-tafiyen taurari.
Bisa wannan kalandar ce, ake fara shiga sabuwar shekara a lokacin sanyi, wato a yayin da ake hutu bayan kammala girbin amfanin gona. Bisa al'adar galibin sassan kasar Sin, ana fara shagulgulan bikin bazara ne a ran 23 ko 24 ga watan sha biyu bisa kalandar wata. Galibin iyalin Sinawa su kan fara tsaftace dakunansu, wato kawar da dukkan tsoffin abubuwa marasa kyau daga gida, sannan a yi bikin girmama manzon dafa abinci.
Bugu da kari, a daren ranar 30 ga watan sha biyu, bayan an ci abinci masu dadi da dare, kusan dukkan iyalai su kan yi hira suna jiran gari ya waye domin murnar shiga sabuwar shekara, wato ranar 1 ga watan farko na sabuwar shekara. Bayan gari ya waye a safiyar ranar 1 ga watan farko, matasa su kan tafi gidajen tsoffi domin nuna musu girmamawa. Saboda ci gaban zamani, yanzu karin Sinawa na amfani da lokutan hutun bikin bazara domin zuwa yawon shakatawa wasu sassa na duniya. Duk da hakan babbar manufar wannan biki mai muhimmanci ga Sinawa, ba ta sauya ba a tsawon shekaru masu yawa, wato haduwa da iyalai bayan tsawon shekara, don murnar shigowar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin.
A ko wace shekara Sinawa na amfani da dabbobi 12 domin wakilcin watannin shekara, a bana sabuwar shekarar gargajiya ta Sin shekara ce ta Zomo. Sauran dabbobin da ke alamta shekaru sun hada da Biri, da Rago da Doki, da Maciji, da Bera da dai sauran su. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)