logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a Kaduna

2023-01-25 16:45:16 CMG Hausa

Mahukunta a jihar Kaduna dake arewacin Najeriya, sun ce sojojin kasar sun yi nasarar ceto mutane a kalla 16, yayin samame 2 da suka kaddamar a yankunan kananan hukumomin Birnin Gwari da Igabi dake jihar.

Da yake tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gidan jihar ta Kaduna Samuel Aruwan, ya ce dakarun sojin kasar su kaddamar da samamen ne, bayan an shaida musu aukuwar harin wasu ‘yan bindiga a sassan kananan hukumomin biyu.

Yayin dauki ba dadi da ‘yan bindigar, sojojin sun hallaka 3 daga cikin su, kuma an garzaya da mutanen da suka jikkata, cikin wadanda aka ceto zuwa asibiti.  (Saminu Alhassan)