logo

HAUSA

Liu Xiabing dake kokarin raya sanaar saka da ake amfani da gora da ta samu sabuwar damar ci gaba

2023-01-24 18:05:39 CMG Hausa

Liu Xiabing mai shekaru 31 da haihuwa, ‘yar asalin garin Pingnan na gundumar Lingshan ta larin Guangxi dake kudu maso yammacin kasar Sin ce. Kayayyakin da ake sakawa da gora na Lingshan sanannu ne, kuma ana sayar da su a kasashen waje, kuma a da sun taba kasancewa tushen samun kudin shiga na jama'ar wurin.

Bayan rikicin hada-hadar kudi da ya barke a shekarar 2008, sana’ar saka da ake amfani da gora ta Lingshan, ita ma ta soma komawa baya sannu a hankali. Amma, Liu Xiabing ba ta taba yin la’akari da yin watsi da sana’ar ba. Tana kallon yadda gyalen gora ke juyawa a karkashin yatsan kakannin ta, kuma ba a dauki lokaci mai tsawo ba suka zama kwanduna ko kwandunan kura. Ta tuna cewa mahaifinta ya fara aikinsa a matsayin mai sana'a da hannu daga sakar hular gora, daga baya, bayan da iyalin suka fara sana’ar sakar ta amfani da gora, kayayyakin cinikayyar da suka kera da sayar su ne kayayyakin da ake bukata a zaman rayuwar yau da kullum.

Mahaifinsa ya ce, sana’ar ta yi kama da yadda rana ke faduwa, amma Liu Xiabing ba ta yarda da haka ba, har ma ta yi ta kokarin farfado da sana’ar. Ta yi fama da rashin nasara da yawa, kuma a yayin da take cikin yanayi mafi muni, bashin da ta ci, ya kai kusan miliyan biyu. Wata rana, lokacin da ta ke sayar da kayayyaki kai tsaye ta yanar gizo, maganganun da masu kallo suka yi sun sanya ta samu wata hanyar farfado da sana’arta ta sakar da ake amfani da gora. Ta yi tunanin cewa, idan mutane ba sa bukatar wata hular da aka saka da gora, watakila za su bukaci wani gidan kyanwa da aka saka da gora. Bayan ta gaza raya sana’arta har sau da dama, a karshe dai ta kaddamar da wani kayan cinikayya mai samun karbuwa kwarai da gaske wato gidan kyanwa, kuma ana iya sayar da irin wannan gidan kyanwa kusan dari biyu a kowace rana, inda ta samu jerin oda masu yawa har bayan tsawon watanni biyu.

Daga baya kuma, Liu Xiabing ta soma tsara wasu kayayyakin da suka shafi batun kyanwa, ban da gidan kyanwa, akwai su jakar ajiye kyanwa, kayan wasan na kyanwa da dai sauransu. A cewarta, “Ban san inda bukatun jama’a za su biyo baya ba, amma ina so in kama wannan damar in nemi wata hanyar cigaba, ga wannan sana’ar gargajiya ta saka da ake amfani da gora.”

Tun da Liu Xiabing ke karamar yarinya, ta iya gano nau'ikan kayan sakar da ake amfani da gora a ko'ina a cikin gidan su, kamar su kwandunan ’ya’yan itace, kwandunan abinci, kwandunan kura... Abin da ya fi zama ruwan dare a gidan shi ne hular gora, wanda shi ne abu na farko da mahaifinta ya koya, bayan ya soma shiga masana’antar saka. Abubuwan da aka saka da gora suna da juriya, da dorewa, kuma ba su da tsada, hakan ya sa su kasance kayan gida da suka fi samu karbuwa a wancan lokacin.

A garin Pingnan, kusan kowane iyali ya san yadda ake saka da gora, wanda kuma ya kasance aiki ga yawancin mutane don ciyar da iyalansu.

Karkashin gado, da inganta sana’ar saka da masu sana'a zuriya daga zuriya suke yi, yanzu kayayyakin saka da gora na Lingshan ya shahara sosai a duniya. Masu saye suna ta shiga garin Pingnan, kuma suna sayar da kayayyakin da aka saka da gora zuwa duk fadin kasar Sin da ma kasashen waje. Liu Xiabing ta tuna da cewa, a lokacin kuruciyarta, danginta sun tsunduma cikin harkokin kasuwancin waje, na sayar da kayan saka da ake amfani da gora, saboda haka, iyalinta na rayuwa sosai kuma ba sa bukatar damuwa game da kudi.

 Amma, komai ya sauya bayan barkewar rikicin kudi a shekarar 2008. Odar ciniki daga kasashen waje ta bace sannu a hankali, tsoffin abokan cinikayyarsu ko dai sun canza ayyuka, ko kuma sun fita daga kasuwanci, haka ma iyalin Liu Xiabing sun ya yi asarar kashi 80% na hanyoyin samun kudin shiga. Sakamakon haka, matsayin zaman rayuwarsu ya ragu sosai, mahaifinta na gajiyawa a ko wace rana. Da ganin haka, sai Liu Xiabing ta gabatar da bukatarta ta koyon fasahar saka, amma mahaifin ta ya ki bukatar a kai a kai. Saboda a ganinsa, aikin nan na wahala ne kwarai, baya ga haka kuma, sana’ar ba ta da makoma mai kyau.”

Tun daga wannan shekarar, sana'ar saka da ake amfani da gora a garin Pingnan ta soma ja da baya sannu a hankali, ya zuwa shekarar 2015, babu masu sana'ar da yawa a garin. Wasu mutane suna aiki a waje, wasu kuma suna aikin noma a gida. Yayin da dazuzzukan gora a cikin tsaunuka ke girma sosai, sana'ar saka dake amfani da gora a Lingshan na raguwa sannu a hankali, kuma mutane kadan ne suka damu da hakan.

Liu Xiabing ta kasance tana kiyaye masana'antar saka dake amfani da gora a ko da yaushe. Bayan ta kammala karatu, daga shekarar 2009 zuwa ta 2015, a cikin shekarun bakwai, ta yi kokari sau da yawa don komawa garin Pingnan, don farfado da fasahar saka dake amfani da gora, amma sau da yawa ta kasa.

A shekara ta 2016, ta sake komawa garinsu, kuma ta fara kokarin yin amfani da yanar gizo don sake gina kasuwancin iyalinta na gudanar da cinikayyar waje. A wannan karo, abokan ciniki sun fara dawowa sannu a hankali, kuma odar da ta samu sun karu a hankali. Sakamakon bukatun da ake da su, iyalin Liu ya zama jagora wajen farfadowar fasaha da sana’ar kasa da ake amfani da gora ta Lingshan. Mahaifin Liu Xiabing, Liu Jiasheng, shi ma ya zama wakilin magajin gadon "Fasahar saka da ake amfani da gora ta Lingshan".

Amma, ba cikin sauki ba ta gudanar da wannan aikin, saboda ta dauki matakai da yawa wadanda ba su dace da halin da take ciki ba, don bude kantin sayar da kaya ta yanar gizo, don haka, ta sake yin kasa, har ma bashin da ta ci ya kai kusan RMB miliyan 2.

To, yaya za ta yi? Kuma ta yaya za ta kyautata irin halin da iyalinta ke ciki? Me ya sa aka ce batun Kyanwa ya ba ta damar farfado da cinikayyar iyalinta, har ma duk sana’ar saka da ake amfani da gora ta garinsu? Masu sauraro, a cikin shirinmu na mako mai zuwa, za mu ci gaba da kawo muku labarin game da Liu Xiabing.