logo

HAUSA

Yadda ‘yan kasashen Najeriya da Nijar ke murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin

2023-01-24 14:30:59 CMG Hausa

Kwanan nan wato ranar Lahadi 22 ga watan Janairu, rana ce ta farko a cikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta al’ummar kasar Sin, wato shekarar Zomo. A halin yanzu al’ummar kasar na bukukuwa kala-kala domin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiyarsu.


Wakilin mu Murtala Zhang ya samu damar zantawa da wasu daga cikin ‘yan kasashen Najeriya da Nijar dake zaune a wurare daban-daban na kasar Sin, don jin ta bakin su game da yadda suke shagulgulan murnar shiga sabuwar shekara tare da mutanen kasar Sin, gami da fahimtar su kan al’adun dake tattare da wannan biki, wanda ya kasance biki mafi kasaita ga al’ummar kasar. (Murtala Zhang)