logo

HAUSA

Kungiyoyin fararen hula na taka rawar a zo a gani ga ci gaban jamhuriyar Nijar

2023-01-24 22:34:10 CMG Hausa

A Nijar, kungiyoyin fararen hula  na taka muhimmiyar rawa wajen daidaita tafiyar jagorancin kasa, wannan kuma tun bayan babban taron kasa shekarar 1991. Ko da yake fiye da shekaru 30 sun wuce, amma kuma duk da haka aikin wadannan kungiyoyi bai canja ba har zuwa wannan lokaci, bisa ga gwagwarmayarsu ta ganin ’yan kasa sun more jagoranci na-gari. Daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijar wakilinmu Maman Ada ya hada mana wannan rahoto.

Bisa tanade tanaden kundin tsarin mulki na galibin kasashen duniya, kungiyoyin fararen hula na kasancewa ginshiken dorewar demokaradiyya da kuma tabbatar da kare hakkin dan adam, su ne ke zama madubin duba ci gaba. A Nijar wadannan kungiyoyin fararen hula  na taka muhimmiyar rawa wajen daidaita tafiyar kasa, tun bayan babban taron conference nationale souveraine a shekarar 1991. Fiye da shekaru 30 ke nan, aikin wadannan kungiyoyi bai canja ba. Nafiou Wada, babban mai shiga tsakani na kawancen kungiyoyin fafaren hula na CUAC. Ya ce tafiyar kasa ta yi kyau dole sai da tsarin mulki na gari:

"Kundin tsarin mulki na kasarmu Nijar, ya kamata a ce shi ne yake tafe da demokaradiyya, kuma cewa hakkin dan adam ya kamata a kare shi, musamman ma idan kuka duba kuka gani, rayuwa tana da tsada, muna cewa gwamnati ta bi sannu, nan a gyara shi, domin yau idan aka gyara, an gyara tafiyar demokaradiyya, an gyara tafiyar kasarmu ta Nijar."

Anda Garba Moussa, shugaban kungiyar matasa domin raya Nijar na RJRN, na ganin ya zama wajibi ga ’yan kasa nasu ba da hadin kai:

"Bisa ga haka, muka ga bana ya kamata mu zabi wannan launi na gudunmmawar da ya kamata ’yan kasa su bada gaba daya, su bada wajen girka zaman lafiya musammun ma yan farar hula. Kun gani duk batun da muka yi shi ne wanda muka yi kira, mukakira ga ’yan kasa gaba daya su kama ma gwamnati."

Shi kuma Abou Zeidi Sanoussi Abdoul Aziz, shugaban zartarwa na kungiyar MOJEDEC, cewa ya yi nauyi ya rataya ga kungiyoyin fararen hula da su kara wayar da kan ’yan kasa:

"Domin su san mene ne kasa, mene ne tafiyar kasa, mene ne dokokin da suka kamata, mene ne ’yancinsu kuma mene ne ya kamata su yi domin a ga sun kawo tasu gudunmuwa gwamnati ita ke da nauyin kome."

Kome ake dai ciki, kungiyoyin fararen hula na rike matsayinsu na kasancewa kunnuwa da idon ’yan kasa a duk lokacin da gwamnati ta raste daga bisa hanyarta. (Mamane Ada)