logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 662 a sassan Najeriya

2023-01-24 18:19:45 CMG Hausa

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, (NEMA) ta bayyana cewa, mutane 662 ne suka mutu, yayin da wasu sama da miliyan 2.4 suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na kasar a shekarar 2022.

Babban darektan hukumar Mustapha Habib Ahmed ne ya bayyana hakan jiya Litinin, a yayin wani taron horar da dabarun tunkarar bala’o’i da aka gudanar a Abuja, babban birnin kasar, Ahmed ya bayyana bala’in ambaliyar ruwa na shekarar 2022, a matsayin wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Najeriya.

A nasa jawabin, daraktan kula da ma’aikatan hukumar NEMA, Musa Zakari, ya bayyana cewa, yadda sauyin yanayi ke canjawa cikin sauri, ya haifar da yawaitar bala’o’i a fadin kasar nan. Yana mai cewa, manufar horon, ita ce baiwa jami’an hukumar ta NEMA karin ilimi kan yadda za a magance bala’o’i.(Ibrahim)