Kayayyakin da aka sarrafa da garin alkama
2023-01-24 16:12:46 CMG Hausa
Kayayyakin da aka sarrafa da garin alkama ke nan, wadanda suka samu matukar karbuwa wurin masu sayayya musamman a lokacin bikin bazara da yanzu haka al’ummar Sinawa ke yi, bikin da ke alamanta shiga wata sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyarsu.
Kasar Sin na da tsawon tarihi na dubban shekaru wajen sarrafa irin kayayyaki, wanda har ya zama wani bangare na al’adun kasar. Ana yawan noman alkama a arewacin kasar Sin, don haka, a kan sarrafa irin kayayyaki da garin alkama, a yayin da a kudancin kasar, a kan sarrafa su da garin shinkafa, sakamakon yadda ake yawan noman shinkafa a bangaren kasar.(Lubabatu)