logo

HAUSA

Yajin aikin da ma’aikatan NAHCO ke yi ya kawo cikas ga zirgar-zirgar jiragen sama a Najeriya

2023-01-24 16:00:23 CMG Hausa

Kamfanonin jiragen sama a Najeriya, sun sanar da cewa, an dakatar da zirga-zirgar jiragen sama jiya Litinin, bayan da ma’aikatan hukumar kula da sufurin jiragen saman kasar suka fara wani yajin aikin na neman karin albashi.

Kamfanin Air Peace, wanda ke da jirage mafi yawa a Najeriya, da kuma karamin kamfanin Dana Air, ya ce yajin aikin da hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama ta Najeriya NAHCO ke yi, yana kawo tsaiko a fannin tashin jiragen. yana mai fatan za a hanzarta magance matsalar. Kuma lamarin ya kawo tsaiko ga jigilar fasinjoji da ma kayayyaki.

A makon jiya ne dai, kungiyar manyan ma’aikatan sufurin jiragen sama ta Najeriya, ta fitar da sanarwar cewa, mambobinta za su fara yajin aiki daga ranar Litinin, don matsawa NAHCO neman karin albashi.(Ibrahim)