logo

HAUSA

Sakataren MDD ya nuna bakin ciki da harbin da aka yi a California

2023-01-24 15:55:48 CMG Hausa

Mai magana da yawun babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya bayyana cewa, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi matukar kaduwa tare da nuna alhini, game da harin da aka kai a dandalin shakatawa na Monterey Park da ke jihar California ta Amurka.

Mahukuntan yankin sun bayyana cewa, mata 5 da maza 5 ne suka gamu da ajalinsu, yayin da wasu mutane 10 kuma suka samu raunuka, sakamakon harbin na ranar daren Asabar da aka yi a birnin Monterey Park mai tazarar kilomita 16 gabas da birnin Los Angeles,  Adadin wadanda suka mutu ya zuwa jiya Lahadi, ya karu zuwa mutane 11.

Mai magana da yawun babban jami’in na MDDr ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, Guterres yana mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalai da kuma masoyan wadanda lamarin ya shafa, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Sanarwar ta kara da cewa, babban sakataren MDDr ya kuma bayyana cewa, yana tare da Amurkawa masu asalin Asiya dake zaune a Amurka.(Ibrahim)