logo

HAUSA

An kaddamar da tashar jirgin ruwa dake Lekki a jihar Legas

2023-01-24 12:02:56 CMG Hausa

A ranar Litinin 23 ga wata, shugaban kasar tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara amfani da tashar jirgin ruwa dake yankin masana’antu na Lekki a jihar Legos dake yankin kudancin kasar.

Yayin bikin, shugaban kasar yana tare da gwamnan jihar Legos Babajide Sanwo-Olu da ministan sufuri Mu’azu Sambo da kuma jakadan kasar Sin a Najeriya Cui Jianchun.

Daga Tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ita dai wannan tashar jirgin ruwa, an bayyana ta da cewa ita ce tasha mafi zurfi a tsakanin tasoshin jiragen ruwan dake Najeriya, kuma an fara aikin ta ne tun a ranar 15 ga watan Junin 2020 karkashin kulawar kamfanin kasar Sin wato China Harbours.

Tashar wadda aikin ta ya lankwame tsabar kudi har dala biliyan 1.5 wanda aka karbo bashi daga bankin bunkasa ayyukan ci gaba na kasar Sin, za ta taka rawa sosai wajen shige da fice na kayayyaki a tsakanin kasashen Afrika dake yankin Sahara.

Da yake jawabi lokacin bikin kaddamar da tashar, gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya tabbatar da cewa, “Mai girma shugaban kasa wannan aiki, aiki ne na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Legas da ta tarayya da kuma kamfanonin ’yan kasuwa, kuma muna farin cikin cewa wannan aiki an fara shi ne a lokacinka kuma aka kammala shi a lokacinka, irin jiragen ruwan da za su rinka zuwa wannan tasha sun ninka har sau 4 a girma kan wadanda suke sintiri a tasoshin ruwan Apapa da Tincan island. Wanann babbar tasha ce da za ta samar da dubban kafofin ayyukan yi, kuma dole mu godewa abokanan huldarmu da muka yi aiki tare musamman ma jakadun kasashen China da Faransa da Singaphore da ma sauran hukumomin daban daban da suka yi aiki ba dare ba raba wajen tabbatuwar wannan aiki.”

Shi kuwa da yake nasa jawabin, Jakadan kasar Sin a Najeriya Mr Cui Jianchun farawa ya yi da cewa, “Wannan rana ce mai mutukar mahimmanci tsakanin kasashen Najeriya da kasar Sin, zan fara da godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa sakon taya murna na sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin da ya aikewa shugaba Xi. Bayan haka ina son na shaida maka cewa wannan sabuwar tasha ta Lekki wani ruhi ne na bunkasar tattalin arziki ba wai kawai ga jihar Legas ba har ma ga kasa baki daya. Mai girma shugaban kasa kada Najeriya ta damu da batun biyan bashin da ta karbo domin gudanar da wannan aiki, kasar Sin na son ku dauki aikin a matsayin wani jari da zai rinka samar maku da kudade shiga ta hanyar haraji da za a rinka karba. Ina kuma fatan cewa wannan kamfani namu zai gudanar da makamancin wannan aiki a sauran sassan Najeriya. Muna godiya sosai shugaban kasa.”

Daga Tarayyar Najeriya, Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)