logo

HAUSA

Burkina Faso ta yanke yarjejeniyar tsaro da Faransa

2023-01-23 16:46:38 CMG Hausa

Gwamnatin Burkina Faso, ta yanke yarjejeniyar jibge dakarun sojin kasar Faransa, tare da umartar sojojin na Faransa da su fice daga kasar.

Kamfanin dillancin labarai na kasar AIB ya rawaito cewa, bisa sanarwar da gwamnati ta fitar a ranar Laraba, an tanadi baiwa dakarun na Faransa umarnin kawo karshen ayyukan su, tare da ficewa daga kasar cikin wata guda, a matsayin matakin kawo karshen yarjejeniyar tsaron da sassan biyu suka kulla a ranar 17 ga watan Disambar 2018.

Umarnin gwamnatin Burkina Faso, ya zo ne a gabar da mahukuntan kasar ke fama da zanga-zangar al’ummar kasa, dake kiran a umarci dakarun na Faransa su fice daga kasar.

A ranar Juma’a ne dubban masu zanga zanga suka bazama kan titunan birnin Ouagadougou, fadar mulkin kasar, inda suka rika bayyana bukatar su ta a kori jakadan Faransa, da dakarun sojojin Faransa dake cikin kasar.  (Saminu Alhassan)