logo

HAUSA

Tun daga yau Litinin ‘yan Najeriya za su iya canza takardun Naira da sababbi

2023-01-23 16:21:05 CMG Hausa

Babban bankin tarayyar Najeriya CBN, ya sanar da cewa, tun daga yau Litinin 23 ga watan nan, al’ummar kasar za su iya canza tsoffin takardun kudin Naira da sababbi, kuma za’a daina amfani, da kuma yin musanyar tsoffin takardun kudin kasar a karshen watan nan na Janairu.

A watan Oktobar bara ne CBN ya sanar da shirin sake fasalin takardun Naira 1000 da 500 da 200, a wani kokari na mayar da takardun kudaden kasar da ba sa shiga bankuna, da magance hauhawar farashin kayayyaki.

CBN ya ce, mutanen dake zaune a yankunan karkara, da kuma wadanda ba sa iya samun hidimar hada-hadar kudi yadda ya kamata, za su iya canza takardun kudin Naira har dubu 10 ga duk mutum guda, ta hanyar kaiwa bankuna ko dillalai, ba tare da bukatar bude asusun banki ba. (Murtala Zhang)