logo

HAUSA

Najeriya ta tabbatar da harbuwar mutum 105 da zazzabin Lassa

2023-01-23 17:08:02 CMG Hausa

Mahukunta a Najeriya, sun ce cikin mutum 369 da aka tantance, an tabbatar da harbuwar mutum 105 da zazzabin Lassa, a tsakanin ranaikun 2 zuwa 15 ga watan nan na Janairu.

Da yake karin haske game da hakan, shugaban cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar Ifedayo Adetifa, ya ce an tabbatar da bullar cutar ne a yankuna 30 na jihohin kasar 10. Jami’in ya ce jihohin dake kan gaba a fama da cutar su ne Edo da Ondo dake kudanci, sai kuma jihar Bauchi ta arewa maso gabashin kasar.

Alkaluman hukumomin lafiyar Najeriya sun nuna cewa, yawan cutar Lassa da aka samu a jihohin 3, ya kai kaso 84 bisa dari, na jimillar ta da aka samu a kasar baki daya.

Tun daga farkon shekarar bara zuwa watan Nuwamba, adadin mutanen da cutar Lassa ta hallaka a Najeriya ya kai sama da mutum 170, cikin mutane kusan 1,000 da aka tantance, yayin da fannin kiwon lafiyar kasar ke matsa kaimin rage yaduwar annobar. (Saminu Alhassan)