logo

HAUSA

An nuna shagalin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiyar kasar Sin da CMG ya tsara a Afirka

2023-01-23 16:13:01 CMG Hausa

Tun daga ranar 20 ga wata ne, aka fara nuna shagalin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiyar kasar Sin, wato shekarar Zomo, wanda babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG ya tsara, a kasashen Afirka, a wani kokari na gabatar da wasanni masu kayatarwa ga al’ummar Afirka, da ‘yan kasar Sin dake zaune a wuraren.

A ranar 20 ga wata, an yi bikin kunna fitilu masu kyan-gani, don murnar shiga sabuwar shekarar gargajiyar kasar Sin, wanda CMG ya tsara a babban ginin hedikwatar bankin kasuwanci na kasar Habasha, wanda ya zama tamkar alama a birnin Addis Ababa, al’amarin da ya zama karo na farko da CMG ya shirya irin wannan bikin kunna fitilu, mai taken murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya a nahiyar Afirka.

Daga bisani a ranar 21 ga watan nan, wadda ita ce jajibirin sabuwar shekarar Zomo, an gabatar da shagalin CMG, na murnar shiga sabuwar shekara kai-tsaye a wasu wurare takwas dake Afirka ta Kudu, gami da Kenya, abun da ya baiwa Sinawa dake wajen damar kallon shirye-shirye masu kayatarwa, duk da cewa akwai nisa sosai tsakanin Sin da Afirka. Haka kuma, al’ummar nahiyar Afirka sun samu damar kara fahimtar al’adun gargajiyar kasar Sin.

A ranar kuma, an gabatar da shirin tallata shagalin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiyar kasar Sin da CMG ya tsara a Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya, inda jama’ar Kenya, gami da Sinawa dake zaune a wurin suka yaba sosai.

Sai kuma a ranar 22 ga wata, wadda ita ce ranar farko a sabuwar shekarar Zomo, a karo na farko, an nuna wasu zababbun shirye-shirye masu kayatarwa, na shagalin murnar shiga sabuwar shekarar Zomo a wurare daban-daban dake kasar Habasha, al’amarin da ya gabatar da kyawawan al’adun gargajiyar kasar Sin ga jama’ar Habasha. (Murtala Zhang)