logo

HAUSA

An sako mata da yara sama da 60 da aka sace a Burkina Faso

2023-01-22 17:21:25 CMG Hausa

Rundunar sojin Burkina Faso, ta ceto mata da yara 66 da aka sace a farkon watan nan, a yankin Sahel na kasar.

Wasu ‘yan bidiga da ba a san ko su wanene ba ne suka sace matan, cikin su har da jarirai 4, a tsakanin ranakun 12 da 13 ga wannan wata, a kusa da garin Arbinda na yankin.

Gidan talabijin na RTB na kasar ya ruwaito cewa, wani samamen dakarun tsaro ne ya kai ga ceto su a ranar Juma’ar da ta gabata a yankin arewa maso tsakiyar kasar, inda aka kai su birnin Ouagadougou. (Fa’iza Mustapha)