logo

HAUSA

Yawan mutanen da suka kalli shagalin bikin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiyar kasar Sin da CMG ya gabatar ta hanyoyi daban-daban ya zarce biliyan 11

2023-01-22 20:04:53 CMG Hausa

Jiya Asabar shi ne jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta al’ummar kasar Sin, wato shekarar zomo, inda babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar, ko kuma CMG a takaice, ya gabatar da wani gagarumin shagalin murnar ranar, dake kunshe da wasanni masu burgewa, da sabbin fasahohi masu ci gaba, da kade-kade da raye-raye masu jawo hankali.

Ya zuwa karfe 2 na asubahin yau Lahadi 22 ga wata, gaba dayan masu kallon shagalin ta hanyoyi daban-daban ya zarce biliyan 11, ciki har da kaso 50.51 bisa dari na mutane masu shekaru 15 zuwa 44 da haihuwa, kuma yawan mutanen da suka kalli shagalin kai-tsaye ta hanyar sadarwar intanet, da kuma yawan mutanen da suka kalli shagalin a kasashen ketare, duk sun kai matsayin koli a tarihi. (Murtala Zhang)