logo

HAUSA

Kasar Sin na aiwatar da manufofin diflomasiyyarta don biyan bukatun al’umma

2023-01-22 20:02:53 CMG Hausa

Kwanan baya wato ranar 8 ga watan Janairun shekarar da muke ciki, aka soma aiki da wasu jerin matakai na zirga-zirgar mutanen gida da na waje a kasar Sin, al’amarin da ya jawo hankalin kasa da kasa sosai, inda a cewar kafafen yada labarai, sabon kokari ne da kasar Sin ta yi domin tabbatar da cewa, an aiwatar da manufofin diflomasiyyar kasar daidai domin biyan bukatun al’umma.

A bara wato shekara ta 2022, annobar COVID-19 ta ci gaba da yaduwa a duk fadin duniya, kana, duniya ta kara fuskantar sauye-sauye masu sarkakiya. Duk da haka, kasar Sin ta ci gaba da aiwatar da manufofin diflomsiyyarta domin tabbatar da muradun jama’ar kasar.

A farkon shekara ta 2022, rikicin kasar Ukraine ya barke, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a tabbatar da tsaron kowane dan kasar dake waje. A ranar 28 ga watan Fabrairun bara, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta fara aikin janye ‘yan kasar daga Ukraine. Kuma sakamakon kokarin da aka yi, ‘yan kasar Sin sama da 5200 sun janye jikinsu daga Ukraine zuwa kasashe makwabtanta.

A bara kuma, kasar Sin ta yi nasarar shawo kan wasu al’amuran duniya na ba-zata, da yin gargadi cikin lokaci, da gudanar da ayyukan kwashe ‘yan kasar daga yankuna masu hadarin gaske, da kuma kokarin kubutar  da mutanen kasar da aka sace. A dayan bangaren kuma, domin shawo kan yaduwar annobar COVID-19, gwamnatin kasar Sin ta yiwa jama’ar ta sama da miliyan 4.6 dake kasashe 180 alluran riga-kafin cutar, tare kuma da taimakawa ‘yan kasar dake fama da matsaloli dawowa gida.  (Murtala Zhang)