COVID-9 ta rage matsakaicin tsawon ran Amurkawa shekaru 2 a jere
2023-01-22 06:14:32 CMG Hausa
Cibiyar dakile da kandagarkin cututtuka ta kasar Amurka CDC ta kaddamar da rahoto a kwanan baya cewa, a shekarar 2021 da ta gabata, matsakaicin tsawon ran Amurkawa ya ragu da kusan shekara guda kan shekarar 2020, adadin da ya ragu cikin shekaru 2 a jere. A cewar rahoton, babban dalilin da ya sa hakan shi ne yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19.
Kamfanin dillancin labaru na The Associated Press, wato AP a takaice ya ruwaito cewa, a shekarar 2020 da 2021 da annobar cutar COVID-19 take yaduwa, matsakaicin tsawon ran Amurkawa ya ragu da kusan shekaru 3 a cikin shekaru 2. Raguwar da aka taba samu tun a lokacin yakin duniya na 2.
Rahoton da sashen kididdigar yanayin lafiyar al’ummar Amurka karkashin inuwar CDC ya nuna cewa, a shekarar 2021, matsakaicin tsawon ran Amurkawa ya kai shekaru 76.1 a duniya, adadin ya kai shekaru 77 a shekarar 2020, wanda ya ragu da kusan shekaru 2 bisa na shekarar 2019. Tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021, matsakaicin tsawon ran Amurkawa ya ragu da shekaru 2.7. A ciki kuma, matsakaicin tsawon ran Amurkawa maza ya ragu da shekaru 3.1, zuwa shekaru 73.2 a duniya, yayin da matsakaicin tsawon ran Amurkawa mata kuma ya ragu da shekaru 2,3, zuwa shekaru 79.1 a duniya.
Matsakaicin tsawon ran mutane, yana daya daga cikin muhimman ma’aunan lafiyar jama’a.
Rahoton ya yi bayani da cewa, yaduwar annobar COVID-19, ta kasance babban dalilin da ya takaice matsakaicin tsawon ran Amurkawa a shekarar 2021. Sauran dalilai sun hada da hadurra, ciwon zuciya, ciwon hanta da ke addabar mutane cikin dogon lokaci, da kisan kai da dai sauransu.
A watan Afrilun shekarar 2022 ne CDC ta kaddamar da rahoton cewa, a shekarar 2021, karo na 2 ke nan a jere annobar COVID-19 ke zama dalili na uku da ke haddasa mutuwar Amurkawa, baya ga ciwon zuciya da kuma cutar sankara. Daga watan Janairu zuwa na Disamban shekarar 2021, yawan Amurkawa da suka rasa rayukansu sakamakon annobar cutar COVID-19 da abubuwa masu nasaba da annobar, ya wuce dubu 460 baki daya. (Tasallah Yuan)