logo

HAUSA

A Jamhuriyar Nijar an fara taron koli kan nazarin hanyoyin samar da tsaro a yankin Sahel

2023-01-21 15:38:39 CRI

A ranar Alhamis 19 ga wata, mahukunta a Janhuriyar Nijar suka fara gudanar da taron koli domin lalubo hanyoyin samar da dawamammen zaman lafiya a kasashen dake yankin Sahel.

An dai bude taron ne a Yamai, fadar gwamnatin kasar inda har tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou tare da  wata babbar tawaga suka gana da shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Yayin  taron kolin masu rawa da tsaki sun fara muhawara kan yada tsaro zai inganta a yankin sahel, kuma majalissar dinkin duniya ce ta tsara taron wanda tsohon shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou yake jagoranta.

Taron na zuwa ne kuma a dai-dai lokacin da kasashen yankin Sahel ke fuskanta barazanar ’yan ta'adda.

A ranar Juma'a ne dai shugabanin wannan taron karkashin jagorancin shugaban taron, tsohon shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou suka gana da shugaban kasa Mohamed Bazoum a fadar shi.

Bayan ganawar da suka yi da shugaban kasa ne Dr Donald Kaberuka ya yi wa manema labarai karin bayani kan abin da suka tattauna da shugaban kasar.

“Da farko dai mu soma gaya muku abin da muka tattauna da shugaban kasa Mohamed Bazoum, taronmu na masu ruwa da tsakin kan sha’anin tsaro wanda tsohon shugaban Nijar Issoufou Mahamadou ya jagoranta. Mun zo ne domin daukar shawarwari daga shugaba Mohamed Bazoum kasancewa matsalar tsaro abu ne mai wuyar lamari a yankin Sahel ko ma duniya baki daya. Mun zo ne domin tattauna wannan lamarin da majalisar dinkin duniya da kungiyar tarayya Afrika da Cedeao ko Ecowas domin mu yi nazari da hukumomin Nijar da kungiyoyin kare hakkin dan Adam da duk wadanda abin ke shafa kuma mun ba shugaban shawarwarinmu da abin da muke ganin zai magance matsalar ta'addanci kuma mun gamsu da yadda shugaban kasa Mohamed Bazoum ya tarbe mu, kuma ya ba mu shawarwari.”

Taro na kwanaki biyu da za'a yi a nan birnin Yamai ya kunshi gomman mutane domin bullo da dabaru magance matsalar tsaro da yankin Sahel ke fuskanta da ma duniya baki daya. (Abdurrahman Sidi Sha'aibu Dabagi)