logo

HAUSA

An sace wasu ‘yan makaranta 6 a yankin tsakiyar Nijeriya

2023-01-21 16:16:46 CMG Hausa

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta tabbatar da sace wasu yara 6 ’yan makaranta, yayin da suke kan hanyar su ta zuwa makaranta a Jihar Nasarawa dake yankin tsakiyar kasar.

Kakakin rundunar, Ramhan Nansel, ya shaidawa manema labarai a Lafiya babban birnin jihar cewa, yaran dalibai ne na wata makarantar firamare ta gwamnati, ‘yan shekaru tsakanin 7 zuwa 8. Kuma wasu ‘yan bindiga akan babura, da ba a san su ba ne, suka sace su a garin  Alwaza, na Jihar da safiyar Jiya Juma’a.

Ramhan Nansel, ya kara da cewa, ‘yan sanda sun gana da shugabancin makarantar da iyayen yaran, kuma sun tura wani ayarin jami’an tsaro na hadin gwiwa zuwa yankin, domin lalubowa da ceto yaran, yana mai cewa sun fara farautar bata garin.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ba ‘yan sanda duk wasu bayanai da za su taimaka wajen ceto yaran da cafke wadanda suka sace su. (Fa’iza Mustapha)